Aruwan: ‘Yan bindiga sun hallaka wani Makiyayi a gona garin Zangon-Kataf

Aruwan: ‘Yan bindiga sun hallaka wani Makiyayi a gona garin Zangon-Kataf

- Gwamnatin Kaduna ta ce an hallaka wani Makiyayi a yankin Zangon Kataf

- Mr. Samuel Aruwan ya tabbatar da aukuwar wannan lamari a Jihar Kaduna

- Mai girma Gwamna Nasir El-Rufai ya aikawa Iyalin Marigayin da ta’aziyya

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kisan wani Bafullatanin makiyayi wanda yake kiwo a kauyen Matyei, da ke karamar hukumar Zangon Kataf.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya bada wannan sanarwa a wani jawabi da ya fitar a farkon makon nan.

Da yake magana da jami’an tsaro game da wannan abu da ya auku a kasar Atyap, Mista Samuel Aruwan ya bada sunan wanda aka kashe da Ado Hassan.

Kwamishinan ya gana da dakarun sojojin kasa na Operation Thunder Strike, OPTS a ranar Lahadi.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe jarirai a Jihar Kaduna

A jawabin da Samuel Aruwan ya fitar, ya bayyana cewa da jami’an tsaro su ka je wata gona da aka yi wa barna, sai suka samu an kashe wannan makiyayi.

Binciken da aka soma a game da kisan wannan makiyayi ya yi sanadiyyar da aka cafke wasu mutane uku; David Kure, Peter Adamu da Bulus Duniya.

Aruwan ya ce daga baya bincike ya kai ga kama karin mutane: Matthew Peter da Yohanna Chawai.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gidan ya ce an tsare wadannan mutane ana yi masu tambayoyi domin bankado masu laifi wajen wannan kisa.

KU KARANTA: Idan Coronavirus ta cigaba da yaduwa, za mu nemi a rufe gari - PTF

Aruwan: ‘Yan bindiga sun hallaka wani Makiyayi a gona garin Zangon-Kataf
Samuel Aruwan da wasu Jami'ai a Kaduna Hoto: Medium Daga: medium.com/@InsideKaduna
Asali: UGC

Gwamna Nasir El-Rufai ya yi tir da wannan aika-aika, sannan ya aikawa iyalin mamacin ta’ziyya tare da kira ga jama’a su daina daukar doka a hannunsa.

A makon nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito ya na cewa wasu Kungiyoyin kasashen waje su na taimakawa ‘Yan ta’adda a Najeriya.

Ministan yada labarai a madadin shugaba Buhari ya bayyana cewa Amnesty International da kotun ICC suna cikin masu kawowa sojojin kasar matsala.

Lai Mohammed yace barazanar kungiyoyin yana dawo da yaki da ta’addanci da rashin tsaro baya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng