Kaduna: 'Yan bindiga sun kashe jarirai uku da karin wasu mutum 6

Kaduna: 'Yan bindiga sun kashe jarirai uku da karin wasu mutum 6

- Wasu 'yan bindiga sun kai hari akan wata tawagar 'yan biki a daidai Zankoro da ke kan babbar hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna

- Wani shaidar gani da ido ya ce 'yan bindigar sun kashe mutane tara cikinsu har da jarirai guda uku

- Bayan sun kai harin ranar Lahadi, 'yan bindigar sun sake tare hanyar da safiyar ranar Litinin tare da sace dumbin mutane

Akalla mutane tara, cikinsu har da jarirai biyu, suka rasa ransu sakamakon wani hari da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai kan wasu matafiya a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne ranar Lahadi a daidai garin Zankoro da ke kan babbar hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna.

Mukhtar Lawal, Wani mazaunin yankin da ya kawowa mutanen dauki bayan harin, ya shaidawa HumAngle cewa "tawagar 'yan bindigar sun kashe mutane da yawa cikinsu har da jarirai uku yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Biki a Doka, karamar hukumar Birnin-Gwari."

KARANTA: KARANTA: Hotuna: Sheikh Gumi ya ziyarci rugage masu hatsari domin yi wa fulani wa'azi akan haramcin garkuwa da mutane

Sarkin masarautar Gwari, Barista Salisu Haruna, ya koka tare da bayyana cewa "kungiyar 'yan bindiga sun sake tare hanya a daidai Zankoro da misalin karfe tare na safiyar ranar Litinin inda suka yi harbe-harbe kafin daga bisani su sace dumbin mutane da ba'a hakkake adadinsu ba."

Kaduna: 'Yan bindiga sun kashe jarirai uku da karin wasu mutum 6
Kaduna: 'Yan bindiga sun kashe jarirai uku da karin wasu mutum 6 Hoto: Nigeria Airforce
Source: Facebook

Mai martaba Haruna ya kara da cewa mutane shidda da suka samu raunuka suna samun kulawa a asibitin Buruku da ke kan babbar hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.

KARANTA: Shekarau ya ce babu karba-karba a tsarin APC, ya bawa 'yan Nigeria shawara akan zaben 2023

Harin na zuwa ne cikin kasa da sa'o'i 24 bayan wasu 'yan bindiga sun kai jerin wasu hare-hare a kauyukan karamar hukumar Giwa inda suka kashe mutane goma sha hudu tare da kona dukiyar miliyoyi.

Sai dai, a ranar Lahadi da safe, rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta ce 'yan bindigar sun kai harin daukar fansa ne bayan an kona wasu 'yan uwansu uku a kauyukan.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa kimanin mutum 18 ake zargin mahara sun kashe tare da sace wasu matan aure biyu yayin wasu jerin hare-hare a ƙaramar hukumar Giwa dake jihar Kaduna.

A cikin wata sanarwa, Kwamishinan al'amurran cikin gida da sha'anin tsaro, Samuel Aruwa, ya ce farmakin ya faru ne a ƙauyukan Kaya dake da iyaka da Hayin Kaura ta jihar Katsina.

A cewar Kwamishinan, an fara kai hare haren ne tun ranar juma'a lokacin da ake murnar shiga sabuwar shekara, ya kara da cewa cikin waɗanda maharan suka sace harda wata matar aure.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel