PTF na la’akari da maganar shigo da takunkumi domin takaita barkewar COVID-19

PTF na la’akari da maganar shigo da takunkumi domin takaita barkewar COVID-19

- Alamu na nuna za a iya maka sabon takunkumi kwanan nan a Najeriya

- Kwamitin PTF ya ce ‘Yan Najeriya ba su bin sharudan da aka gindaya

- Kwamitin ya ce za a rufe gari idan har Coronavirus ta na yaduwa sosai

Alamu su na nuna cewa za a iya sake garkama takunkumi nan ba da dadewa ba a Najeriya saboda karuwar masu dauke da COVID-19.

Kwamitin da shugaban kasa ya kafa na PTF mai yaki da annobar COVID-19, ya ce mutane ba su bin ka’idoji don haka cutar ta ke ta yaduwa.

Daga cikin matakan da kwamitin zai iya dauka domin ganin an dakile yaduwar wannan cuta ta COVID-19, The Nation ta ce har da rufe gari.

Shugaban kwamitin, Dr. Sani Aliyu, ya bayyana cewa muddin aka cigaba da samun karin masu kamuwa da cutar, watakila a maka takunkumi.

KU KARANTA: Bola Tinubu bai da lafiya ya na asibiti, amma ba COVID-19 ba ce

Da yake magana, Dr. Sani Aliyu, ya ce ta haka ne kurum za a iya shawo kan wannan annobar.

Jaridar ta rahoto Dr. Aliyu ya na cewa: “Idan alkaluma su na tashi, adadin masu cutar ya na yin sama, za mu duba duk matakan da mu ke dasu.”

“Watakila ba za su yi mana dadi ba, abin ba zai kai garkame gari wahala ba” inji kwamitin na PTF.

Shugaban kwamitin ya ke cewa mutane 33 sun mutu a makon da ya gabata a sakamakon COVID-19. “Mu na cewa duk sun mutu a banza kenan?”

KU KARANTA: Rashin tsaro, COVID-19 da sauran matsalolin da za su yi ta addabar Najeriya

PTF na iya la’akari da shawarar sa takunkumi domin takaita barkewar COVID-19
Shugaban PTF na kasa Hoto: Twitter Daga: @DigiCommsNG
Asali: Twitter

“Mun samu mutane 6, 000 dauke da cutar a cikin makon nan da ya wuce. Wannan ya zarce duk abin da mu ka taba samu tun da ake annobar.”

A shekarar da ta wuce kun ji labarin wasu ma'aurata da su ka sa wa jariransu sunan cutar.

Wadannan ma'aurata sun saka wa tagwayen da suka haifa yayin annobar nan suna Corona da Covid, wannan abin mamaki ya faru ne a Indiya.

"An haifesu ne bayan fuskantar matsin rayuwa saboda annobar, don haka ni da mijina muka yanke shawarar sa musu suna mai tarihi." inji Mai jegon.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng