‘Yan sanda sun cafke mutum 18 da ake zargi da tayar da tarzoma a Zamfara

‘Yan sanda sun cafke mutum 18 da ake zargi da tayar da tarzoma a Zamfara

- 'Yan sanda sun cafke wasu da ake zargi da tada tarzoma a Zamfara a yau Lahadi

- Tarzomar ta kai ga lalata dukiya da ya hada da lalata wani bangare na fadar Sarkin Shinkafi

- 'Yan sandan sun yi kira ga jama'a da su kula da 'ya'yansu ko yaushe dan guje wa rigima

Rundunar ‘yan sanda a Zamfara ta kame mutane 18 da ake zargi a kan wani rikici, wanda ya kai ga lalata dukiya ciki har da fadar Sarkin Shinkafi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Muhammad Shehu ya fitar a ranar Lahadi a Gusau.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun yi ruwan bama-bamai kan maboyar ‘yan ta’adda a Borno

‘Yan sanda sun cafke mutum 18 da ake zargi da tayar da tarzoma a Zamfara
‘Yan sanda sun cafke mutum 18 da ake zargi da tayar da tarzoma a Zamfara Hoto: Facebook/Premium Times
Asali: Facebook

“Matasa dauke da bindigogin dane, adduna da sanduna sun lalata fadar Sarkin Shinkafi da wasu gidaje biyu a garin Shinkafi.

“Hadaddiyar rundunar‘ yan sanda da ta sojoji sun mayar da martani cikin sauri kuma sun tarwatsa masu zanga-zangar don kauce wa rusa doka da oda da yiwuwar asarar rayuka da dukiyoyi.

“Mutum 18 da ake zargi da aka kame a yanzu haka suna hannun‘ yan sanda ana yi musu tambayoyi.

KU KARANTA: Aisha Yesufu ta caccaki gwamnatin Buhari a kan kama Sowore

Shehu ya ce "Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Mista Abutu Yaro ya umarci CID na jihar da su fara gudanar da bincike a kan zanga-zangar ba bisa ka'ida ba da nufin gano yadda lamarin ya faru."

Yaro ya gargadi iyaye da masu kula da su kula da 'ya'yansu ko yaushe don hana su shiga cikin ayyukan ta'addanci. (NAN)

A wani labarin, Fusatattun matasa a jihar Katsina a jiya sun fito zanga-zanga tare da rufe manyan tituna sakamakon fusata da garkuwa da mutane tare da harin 'yan bindiga a kauyukansu.

Matasan da suka fito daga kauyuka daban-daban na karamar hukumar Dandume sun rufe babban titin da ke hada yankin da karamar hukumar Funtua ta jihar.

A ranar lahadi jaridar Daily Trust ta gano cewa matasan sun mamaye titin inda suka yi barazana ga gwamnati a kan ta dauka mataki ko kuma su samo hanyar kare kansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel