Sojojin Najeriya sun yi ruwan bama-bamai kan maboyar ‘yan ta’adda a Borno
- Rundunar sojin sama na Najeriya ya samu damar halaka 'yan ta'adda a borno
- Sojoijn sun kai harin bayan samun bayanan sirri ingattace daga majiya mai tushe
- Harin ya jawo ruguje mafakar 'yan ta'addan tare da kashe da yawa a cikinsu
Hedikwatar tsaro ta ce rundunar sojin sama ta Operation Lafiya Dole ta rusa wasu mafakar ‘yan ta’addan, inda suka kashe 'yan ta'addan da yawa a wurare biyu a Borno.
Jami'in yada labarai na bangaren yada labarai na tsaro, John Enenche, a wata sanarwa a ranar Lahadi, ya ce an kai hare-haren ne a ranar Asabar a garuruwan Kote Kura da Bulama Isamari da ke Borno.
KU KARANTA: Boko Haram sun sace ma’aikacin Majalisar Dinkin Duniya a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu
Mista Enenche ya ce, rundunar ta Air Force ta yi amfani da jiragen yaki da kuma jiragen yaki masu saukar ungulu bisa ingantattun bayanan sirri.
Ya ce bayanan sirrin sun gano cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun kafa sansanoni a tsakanin matsugunan biyu inda suke ajiye kayan aikin su tare da shiryawa da kuma kai hare-hare.
A cewarsa, a saman Kote Kura, wani yanki a yankin Bama, jirgin saman NAF ya yiwa 'yan ta'adda da dama dirar mikiya a yankin da aka nufa.
“Harin ya kai ga kawar da yawancinsu tare da lalata gine-gine da wuraren adana kayan aiki, an ga wasu suna cikin wuta.
KU KARANTA: ‘Yan sanda sun kame wadanda ake zargi da yin garkuwa da Bishop din Katolika na Owerri
"A daidai wannan hanyar, a Bulama Isamari, a cikin Timbuktu Traingle, jirgin NAF ya juyo da niyyar aiwatar da abin da ya sa a gaba, ya zira kwallaye daidai wanda hakan kuma ya haifar da kawar da 'yan ta'adda da dama," in ji shi.
A wani labarin, A ƙalla sama da fararan hula 70 ne aka kashe a wasu tagwayen hare-hare da ake zargin yan kungiyar Boko Haram ne suka kai kan wasu ƙauyuka biyu dake ƙasar Nijar kusa da iyaka da kasar Mali.
Kimanin mutum 50 ne aka kashe a ƙauyen Tchombangou sannan 17 suka ji mummunan rauni kamar yadda wani jami'in tsaro ya tabbarwa Reuters ya kuma nemi da a sakaye sunansa, kamar yadda TheCable ta rawaito.
Wata majiya daga wani jami'in harkokin cikin gida na ƙasar ta Nijar da shima ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da an kashe sama da kimanin mutum 30 a Zaroumdareye.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng