Cristiano Ronaldo ya zarce Pele yawan kwallaye bayan ya ci kwallo na 758

Cristiano Ronaldo ya zarce Pele yawan kwallaye bayan ya ci kwallo na 758

- Cristiano Ronaldo ya zura kwallaye biyu a wasansa na farko a 2021

- Hakan na nufin ‘Dan wasan na kasar Portugal ya na da kwallo 758

- Ronaldo ya zarce tsohon ‘Dan wasan gaban da aka yi a Brazil, Pele

‘Dan wasan gaban kungiyar Juventus, Cristiano Ronaldo, ya shiga wannan shekara da kafar dama, bayan ya zura kwallaye biyu a wasansu da Udinese.

Kwallaye biyun da Ronaldo ya yi kumallo da su a farkon shekarar nan sun sa ya zarce Pele a jerin ‘yan wasan da su ka fi kowane kwallaye a tarihin wasan.

Daga lokacin da ya fara wasa a matsayin babban ‘dan kwallon kafa zuwa yanzu, ‘dan wasan na kasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya jefa kwallaye 758 a raga.

Cristiano Ronaldo ya zama na biyu a jerin masu yawan kwallaye, ya na bin tsohon ‘dan kwallon kafan Brazil, Pele wanda ya ci kwallaye 757 kafin ya ajiye wasa.

KU KARANTA: An binciko abin da ya hallaka Maradona

Pele wanda ya bugawa kungiyoyin kwallon kafa na Santos da New York Cosmos tsakanin shekarar 1957 da 1977 ya dade ya na rike da wannan tarihi.

Sai bayan shekaru 43 aka samu wanda ya shafe wannan tarihi da Pele mai shekara 80 ya ajiye.

A wasan Juventus da Udinese na ranar Lahadi ne Ronaldo ya kamo kafar Pele a minti na 31, kafin a tashi wasan ya zura kwallo na biyu, wanda ya kai shi 758.

A wannan wasa da aka yi ne tsohon ‘dan kwallon na Real Madrid ya yi sanadiyyar da Federico Chiesa ya jefa kwallonsa, sai kuma Paulo Dybala ya ci ta hudu.

KU KARANTA: ‘Yan wasan kwallon kafa 14 da su ka yi ritaya a 2020

Cristiano Ronaldo ya zarce Pele yawan kwallaye bayan ya ci kwallo na 758
Pele da Ronaldo Hoto: www.insider.com
Source: UGC

Jaridar SunSport ta ce Josef Bican wanda ya ci kwallaye 759 tsakanin 1931 zuwa 1955 ne kadai ya ke gaba da Ronaldo, ratar kwallo 1 ce rak tsakaninsa da shi.

Idan mu ka dawo gida Najeriya kuma za mu ji cewa an bada sanarwar wani babban 'dan wasan kungiyar Nasarawa United, Muhammad Hussain, ya ɓace.

Shugaban kungiyar Nasarawa Utd, Isaac Danladi ne ya sanar da haka a garin Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa bayan an rasa inda 'dan kwallon ya shiga.

Mista Isaac Danladi ya gargadi duk wani mutum ko kungiya da ke wannan shirin ya yi hattara.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel