Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta sake kara farashin wutan lantarki

Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta sake kara farashin wutan lantarki

- Bayan karin farashin wuta da akayi a Nuwambar 2020, an sake tafka wani karin

- Hukumar NERC ta ce nan da Yunin 2021 za ta kara wani karin kuma

- Yan Najeriya basu gama kokawa kan karin baya ba gashi an samu sabon kari

Hukumar lura da wutan lantarkin Najeriya NERC, ta amince da kara farashin wutan lantarki na kashi 50 kan abinda kwastomomi ke biya yanzu a fadin tarayya, rahoto daga Daily Trust.

Hakan zai shafi kamfanonin raba wutan lantarki 11 dake Najeriya.

Wannan na zuwa ne watanni biyu kacal da kara farashin a watan Nuwamba 2020.

A cewar umurnin waiwayan farashin shekara-shekara da sabon shugaban NERC, Engr. Sanusi Garba, ya rattaba hannu ranar 30 ga Disamba, 2020, kuma aka gani ranar Talata, an fara dabbaka sabon farashin ne fari daga ranar 1 ga Junairu, 2021.

A umurnin mai lamba NERC/225/2020, ta bayyana abubuwan da tayi la'akari da su wajen kara wannan farashi.

A cewar ta, anyi la'akari ne da hauhawar tattalin arzikin 14.9% da akayi a Nuwamba, 2020, da kuma tashin dalar Amurka zuwa N379.4/$1 a karshen Disamba, 2020.

Hakazalika an lura da adadin wutan da aka samu tatsowa, hauhawar tattalin arzikin Amurka na 1.2% da kuma kudin da kamfanonin wutan lantarki zasu yi amfani wajen inganta wutan lantarki

Wannan sabon farashin zai shafi kowa da kowa sabanin na baya da ya togaciye wadanda basu samun wutan lantarki sama da awanni 6 a rana.

Wannan farashin zai kasance daga yanzu zuwa Yunin 2021, kafin kuma aka sake karawa daga Yuni zuwa Disamba 2021, NERC ta bayyana.

KU KARANTA: Iran shirye take ta taimakawa Najeriya wajen kawo karshen ta'addanci, Jakada

Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta sake kara farashin wutan lantarki
Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta sake kara farashin wutan lantarki
Asali: Twitter

KU DUBA: A ranar guda: Mutane 1200 sun kamu da cutar Korona a Litinin

A wani labarin kuwa, fitaccen marubucin Najeriya da ya taba lashe kyautar Nobel, Farfesa Wole Soyinka, ya ce idan har mutum bana son ya zautu, ya rika tsamanin kawai babu gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a kasar.

Amma ya bayyana layin dogo da jiragen kasa na Lagos zuwa Abeokuta a matsayin abin ban sha'awa da ya dace a yi tun da dadewa.

Soyinka ya yi wannan jawabin ne yayin hirar da aka yi da shi a KaftAn TV.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng