COVID-19: Yobe da wasu jihohi 5 da suka amince da bude makarantu

COVID-19: Yobe da wasu jihohi 5 da suka amince da bude makarantu

Yayinda annobar Korona ke ci gaba da haddasa fargaba a kasar saboda tsoron barkewar mugunyar cutar a karo na biyu, wasu jihohi sun sanar tare da amincewa da komawa makarantu.

A tuna cewa gwamnatocin jiha sun rufe makarantun gwamnati da na masu zaman kansu sakamakon yaduwar annobar a kulla-yaumin.

A yanzu Najeriya ta tabbatar da mutum 91,351 da suka kamu da annobar inda 75,699 suka warke sannan 1,318 suka mutu bayan hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta kasa (NCDC) ta sanar da sabbin mutane 1204 da suka kamu a ranar Litinin, 4 ga watan Janairu.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta jero wasu jihohi shida da suka amince da bude makarantu duk da hauhawan yawan masu korona a kullun.

COVID-19: Yobe da wasu jihohi 5 da suka amince da bude makarantu
COVID-19: Yobe da wasu jihohi 5 da suka amince da bude makarantu Hoto: Olukayode Jaiyeola
Asali: Getty Images

1. Jihar Rivers

An umurci dukkanin makarantun gwamnati da masu zaman kansu na Firamare da sakandare a jihar Rivers su bude a ranar Litinin, 4 ga watan Janairu.

KU KARANTA KUMA: Bincike ya nuna yan Najeriya sun fi damuwa da rashin tsaro da talauci fiye da korona

Umurnin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren din-din-din na ma’aikatar ilimi a jihar, Chido Adiele ya saki a ranar Lahadi, 3 ga watan Janairu.

Adiele ya ce an yanke shawarar sake bude makarantun ne domin cimma kalandan da aka wallafa a watan Agustan 2020.

Jihar Rivers na da jimlar mutum 3,602 da suka kamu.

2. Jihar Lagos

A ranar Lahadi, 3 ga watan Janairu, gwamnatin jihar Lagos tayi umurnin cewa dukkan makarantu a jihar su ci gaba da kasancewa a kulle har sai baba-ta-gani saboda yaduwar annobar korona.

Amma sai ta lashe amenta, inda jihar ta sanar da bude makarantu daga ranar Litinin, 18 ga watan Janairu.

Kwamishinan ilimi na jihar, Folasade Adefisayo ce ta sanar da hakan a ranar Litinin, 4 ga watan Janairu.

Cibiyar annobar, Lagas na da mutum 31,973 da suka harbu bayan NCDC ta sanar da cewa Lagos ta samu karin mutum 654 da suka kamu a ranar Litinin.

3. Jihar Nasarawa

Gwamnatin jihar Nasarawa karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Sule ta sanar da cewa makarantu za su bude a ranar 18 ga watan Janairu.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kwamishinar ilimi, kimiya da fasaha, Hajiya Fatu Jimaita Sabo.

4. Jihar Bauchi

Dukkan makarantu, ciki harda manyan makarantu a jihar Bauchi za su bude a ranar 18 ga watan Janairu, maimakon ranar 4 ga watan Janairu kamar yadda kwamishinar ilimi na jihar, Dr Aliyu Tilde ya sanar.

KU KARANTA KUMA: Jerin sunayen jami’o’in Najeriya da suka sanar da ranar komawa makaranta

5. Jihar Ekiti

Gwamnatin jihar Ekiti ta kwamishinan ilimi, kimiya da fasaha, Dr Bimpe Aderiye, ta sanar da cewa batun bude makarantu don zangon karatu na biyu a ranar 18 ga watan Janairu na nan.

Ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin a Ado-Ekiti, babbar birnin jihar.

6. Jihar Yobe

Jihar Yobe karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni bai sanar ba a hukumance amma ya tsegunta batun komawa makaranta a ranar 18 ga watan Janairu, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kwamitin jihar kan korona ta ce za ta sanar da hukuncinta kafin karshen mako.

A gefe guda, mun ji cewa daga karshen watan Maris zuwa Disamban 2020, jami’o’in gwamnati na Najeriya sun rufe saboda yajin aikin da kungiyar malaman ASUU suka tafi.

Bayan tsawon watanni da aka kwashe ana tattaunawa, daga karshe kungiyar malaman sun dakatar da yajin aiki a ranar Laraba, 23 ga watan Disamba.

Sai dai kuma, makarantu basu koma karatu nan take ba saboda dama kasar ta shiga lokaci na bukukuwa wanda ke cike da hutu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel