Allah ya yi wa ƙanin Sarkin Daura rasuwa sakamakon hatsarin mota

Allah ya yi wa ƙanin Sarkin Daura rasuwa sakamakon hatsarin mota

- Abdullahi Umar, kanin Sarkin Daura, Mai martaba Umar Faruk Umar ya riga mu gidan gaskiya

- Umar ya rasu ne sakamakon hatsarin mota da ta ritsa da shi da abokansa biyu a ranar Lahadi a hanyar Katsina/Daura

- Gwamnan Kstaina, Aminu Bello Masari ya tafi fadar sarki don yi masa ta'aziyyar rasuwar kaninsa da sauran mutanen biyu

Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq, ya rasa kaninsa, Abdullahi Umar sanadiyyar hatsarin mota da ta ritsa da shi, The Punch ta ruwaito.

Umar ya rasu ne sakamakon mummunan hsatarin mota a hanyar Katsina/Daura a ranar Lahadi tare da abokansa biyu.

Allah ya yi wa kanin sarkin Daura rasuwa sakamakon hadarin mota
Allah ya yi wa kanin sarkin Daura rasuwa sakamakon hadarin mota. Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kyakyawar amarya ta rasu ana saura sa'o'i 3 a ɗaura aurenta a Katsina

A halin yanzu ba gama samun cikaken bayani kan yadda hatsarin ya afku ba amma Gwamna Aminu Bello Masarri na jihar Katsina a ranar Litinin ya yi wa sarkin Daura ta'aziyyar rasuwar kaninsa.

Mai bada shawara na musamman kan ilimin makarantun gaba da sakandare, Dr Bashir Ruwangodiya da wasu manyan jami'an gwamnati ne suka yi wa gwamnan rakiya zuwa ta'aziyyar.

Sarkin Daura, Umar Faruk Umar, Atoney Janar na Jihar, Barrista Ahmed El-Marzuq da Ambasada Adamu Sai'du ne suka tarbi gwamnan da tawagarsa a fadar sarkin.

KU KARANTA: Mata mai sana'ar wankau ta gina gidan kanta, 'yan Najeriya sun taya ta murna

Gwamna Masari ya kuma ziyarci gidajen sauran mutanen biyu da suka rasu inda ya yi wa iyalansu jaje.

Ya yi addu'ar Alllah ya jikanssu ya kuma bawa iyalansu hakurin jure rashin.

Marigayi Abdullahi Umar ya rasu ya bar matar aure daya da yara takwas da yan uwa da dama ciki har da Sarkin Daura.

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel