Zulum ya aza tubalin gina jami'a mai zaman kanta ta farko a Borno (Hotuna)

Zulum ya aza tubalin gina jami'a mai zaman kanta ta farko a Borno (Hotuna)

- Gwamna Zulum na Jihar Borno ya aza harsashin gina jami'ar Al-Ansar, jami'a mai zaman kanta a jihar Borno ranar Litinin

- Gwamnan ya kuma ce a shirye gwamnatin sa take ta tallafawa duk wani mai son taimakawa bangaren ilimi a jihar

- Dr Muhammad Kyari Dikwa shi ne shugaban gidauniyar Al-Ansar kuma wanda ya samar da jami'ar, ya yabawa gwamnatin Zulum bisa tallafawa bangaren ilimi

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a ranar Litinin ya aza harsashin gina jami'ar Al-Ansar, jami'a ta farko mai zaman kanta a jihar.

Zulum wanda gwamnatin sa ta bada fili mai girman hekta 100 ga gidauniyar Al-Ansar don gina jami'ar, ya kuma umarci da a gina titi mai nisan kilo mita 2.3 da kuma bohol a jawabin da ya gabatar wajen taron.

Zulum ya aza tubalin gina jami'a mai zaman kanta ta farko a Borno
Zulum ya aza tubalin gina jami'a mai zaman kanta ta farko a Borno. Hoto: @vobvoice
Asali: Facebook

Zulum ya aza tubalin gina jami'a mai zaman kanta ta farko a Borno
Zulum ya aza tubalin gina jami'a mai zaman kanta ta farko a Borno. Hoto: @vobvoice
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mata mai sana'ar wankau ta gina gidan kanta, 'yan Najeriya sun taya ta murna

Zulum ya kuma umarci ma'aikatar ilimi mai zurfi da su bibiyi wanda ya samar da jami'ar don ganin yadda gwamnati zata iya ci gaba da tallafawa aikin.

Gwamnan wanda ya jaddada kudirin gwamnatin sa na tallafawa ilimi a jihar, yayi alkawarin tallafawa duk wani mai yunkurin samar da ingantaccen ilimi a Borno.

"A shirye muke mu tallafawa duk wani mutum ko kungiya da ke son hada hannu da gwamnatin mu wajen samar da ingantaccen ilimi a kowane mataki," a cewar Zulum.

Zulum ya aza tubalin gina jami'a mai zaman kanta ta farko a Borno
Zulum ya aza tubalin gina jami'a mai zaman kanta ta farko a Borno. Hoto: @vobvoice
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kyakyawar amarya ta rasu ana saura sa'o'i 3 a ɗaura aurenta a Katsina

A nasa jawabin, wanda ya samar da jami'ar kuma shugaban gidauniyar Al-Ansar, Dr Muhammad Kyari Dikwa, ya bayyana cewa za a fara jami'ar da bangarori biyu.

Dr Dikwa ya yabawa gwamnatin Zulum bisa yadda take tallafawa bangaren ilimi tare da tabbatar da cewa zasu taimaka wajen bada ingantaccen ilimi a jihar.

Zulum ya aza tubalin gina jami'a mai zaman kanta ta farko a Borno
Zulum ya aza tubalin gina jami'a mai zaman kanta ta farko a Borno. Hoto: @vobvoice
Asali: Twitter

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel