'Yan Boko Haram sun kai farmaki sansanin sojoji, sun kashe 7, sun raunata wasu
- 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari sansanin sojojin Najeriya da ke Kuda kusa da Chibok a Jihar Borno
- Sakamakon fafatawa da sojojin suka yi da 'yan ta'addan, sojoji takwas sun riga mu gidan gaskiya, wasu sun jikkata
- Yan ta'addan sun kuma kone kimanin gidaje 40 a kauyen bayan sun sace kayayyakin abinci da dabobin mutanen kauyen
A kalla mutane bakwai ne aka kashe ciki har da sojoji a yayin da wasa da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai hari a sansanin sojoji da ke kudancin Borno a yammacin ranar Lahadi a cewar majiyoyi, Daily Trust ta ruwaito.
An gano cewa 'yan ta'addan sun kai hari a wani sansanin sojoji a Kuda, kusa da Chibok a misalin karfe 4.30 na yamma inda suka yi musayar wuta da sojoji suka kashe shida ciki har wa mai mukamin warrant ofisa.
Wani dan kungiyar 'yan sa kai, Yohanna Bitrus ya ce maharan sun kone gidaje kimanin 40, sun kuma sace ababen hawa uku bayan sun sace kayan mutanen kauyen.
DUBA WANNAN: Zulum ya aza tubalin gina jami'a mai zaman kanta ta farko a Borno (Hotuna)
"Sun zo da yawa suka kai wa sansanin sojoji da ke Kuda hari, sun ci galaba kan sojojin sun kashe sojoji shida sun rautana wasu takwas.
"An kona wata mata a cikin gidanta.
"Sun kuma kona gidaje fiye da 40 bayan sun sace kayayyakin abinci da dabobi.
"Muna rokon gwamnatin tarayya ta tallafa mana cikin gaggawa, muna bukatan karin sojoji da kayan aiki domin tunkarar yan ta'addan," in ji Bitrus.
KU KARANTA: Allah ya yi wa kanin sarkin Daura rasuwa sakamakon hatsarin mota
Wani majiya daga rundunar soji da baya so a ambaci sunansa ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce akwai wasu sojoji takwas a sansanin.
"Eh, an kai wa dakarun mu hari a jiya, sojojin mu sun yi fafata da su sosai amma sun rasa wasu daga cikin sojoji, wasu sun jikkata," in ji majiyar sojojin.
Kauyen Kuda na da nisan kilomita 3 ne daga Chibok.
Kawo yanzu rundunar sojoji bata karyata ko gasgata afkuwar lamarin ba a lokacin hada wannan rahoton.
A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.
Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.
A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng