Siyasar Kano: An yi hannun riga tsakanin Ganduje da Sha'aban Sharada

Siyasar Kano: An yi hannun riga tsakanin Ganduje da Sha'aban Sharada

- Siyasar Jihar Kano na kara daukan zafi a yayin da zaben kananan hukumomi ke kara karatowa

- An samu rabuwar kai a tsakanin bangarorin jam'iyyar PDP a jihar Kano dangane da shiga zaben

- Kazalika, ita ma jam'iyyar APC ta fara fuskantar tarnakin siyasa gabanin matsowar zaben

Honarabul Sha'aban Ibrahim Sharaɗa, mamba a majalisar wakilai ta kasa mai wakiltar ƙaramar hukumar birnin Kano(KMC) ya yiwa gwamna Ganduje wankin babban bargo.

Cikin wani faifan bidiyo mai tsawon minti guda da ɗan majalisar ya wallafa, an jiyo shi yana caccakar gwamnatin Ganduje bisa wasu tsare tsarenta, kamar yadda Freedom Radio da ke Kano ta wallafa.

Sha'aban Sharaɗa ya ce;

"Duk wani fili da ya rage wanda nan gaba za'a yiwa al-umma hidima ana saida shi, a kama makaranta a yanka ace an baiwa wane, a samu asibiti a yanka ace an baiwa wane, a samu masallaci ace an baiwa wane, a samu hanya a yanka ace an baiwa wane, a samu maƙabarta a yanka ace an baiwa wane."

KARANTA: Rufe layukan waya: Yadda za ku duba ko an hada layinku da NIN daga wayoyinku na hannu

Siyasar Kano: An yi hannun riga tsakanin Ganduje da Sha'aban Sharada
Siyasar Kano: An yi hannun riga tsakanin Ganduje da Sha'aban Sharada @Freedomradio
Source: Twitter

"To dan Allah ina za'a je?, me ake so?, me za'a yi da duniya?."

"Mu wallahi tallahi duk wanda ya saurara min baya ƙaunar Allah, mun ja layi, su ma su ja muga wanda zai fi shan wahala."

Sai dai gwamna Ganduje bai yi wata wata wajen maida zazzafan martani ta bakin mai bashi shawara kan al'amurran jama'a, Hon. Fa'izu Alfindiki ba.

KARANTA: Ka farga haka ko mu dauki mataki mai tsauri: Sanatoci sun gaji da yi wa Buhari alkunya

Alfindiki ya ce "a siyasa ni ba sa'an ka bane, ni uban gidanka ne, nine na koyar da kai siyasa, ni na taimaka maka a siyasa."

"Ni nake binka bashi a siyasa, sauran waɗanda ke ƙasa da ni sune sa'anninka a siyasa, amma Allah ya ɗaukaka ka, ya daraja ka, amma ba ka riƙe darajarka da muhimmanci ba."

Tuni dai jama'a da dama suka shiga tofa albarkacin bakunansu a kafafen sadarwar zamani.

Hakan yazo dai-dai lokacin da jam'iyyar APC ke yunƙurin zaɓen ƙanana hukumomi wanda tsagin masu adawa da hamayya suka janye hannunsu ciki.

A ranar 15 ga watan Disamba ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa Shugaban majalisar dokokin jihar Kano da shugaban masu rinjaye sun yi murabus daga mukamansu.

Abdulaziz Garba Gafasa, shugaban majalisar, ya sanar da cewa ya yi murabus a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 14 ga watan Disamba.

Tuni wasu rahotannin su ka wallafa cewa akwai kimanin mambobin majalisar dokokin jihar Kano 12 'yan APC da ke shirin komawa PDP.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel