Rashin Tsaro: Buhari ya yi kira ga daukar matakin bai daya kan 'yan ta'adda

Rashin Tsaro: Buhari ya yi kira ga daukar matakin bai daya kan 'yan ta'adda

- Shugaba Muhammadu Buhari a Nijeriya ya nuna damuwarsa a kan kashe mutane da a ka yi a Nijar

- Shugaban yayi kira ga makotan Nijeriya da su hada karfi domin yakan 'yan ta'adda a yankin

- Buhari ya danganta tashin hankali a Afrika ta yamma da kifar da mulkin Gaddafi

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce "Yanzu ta'addanci ya zama kamar wata muguwar cuta wacce za ta iya yaduwa a kowane lokaci matukar ba a dauki mataki na bai daya ba."

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar ranar Lahadi don mayar da martani kan kisan mutane 70 a garin Zaroumdareye, wani garin kan iyaka tsakanin Jamhuriyar Nijar da Mali da ‘yan bindiga suka yi, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban wanda ya yi Allah wadai da lamarin tare da nuna damuwarsa ga yadda tsaro yake qara tabarbarewa, ya ce wannan wani karin kira ne na daukar matakin bai daya na shugabannin Afirka kan ta'addanci.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Gombe zata dawo biyan ƙarancin albashi nan kusa

Shugaban ya ce: "Na yi matukar kaduwa da yawan mutuwar mutane marasa laifi a hannun wadannan mayaka marasa imani wadanda ba su kula da tsarkin rayuwar dan Adam."

“Muna fuskantar babban kalubale na tsaro saboda mummunan yakin da ake yi na tashin hankali ba gaira ba dalili daga ‘yan ta’adda a yankin Sahel kuma hada kai kawai ne zai iya taimaka mana mu kayar da wadannan mugayen makiya na bil'adama."

Rashin Tsaro: Buhari ya yi kira ga daukar matakin bai daya
Rashin Tsaro: Buhari ya yi kira ga daukar matakin bai daya Hoto: Twitter/@MBuhari
Asali: UGC

Shugaba Buhari ya ce "rashin zaman lafiya a wani yanki na Afirka na da tasiri ga tsaron wasu."

Ya tunatar da cewa "Tabarbarewar zaman lafiya a Libya a shekara ta 2011 yana haifar da matsala mai tasiri ga tsaron wasu kasashen Afirka da suka hada da Najeriya, Nijar, Chadi, Kamaru da sauransu.

Shugaban ya kara da cewa: "Satar kayayyakin makamai na Libya a bayan faduwar Gaddafi ya sanya muggan makamai a hannun 'yan ta'adda da sauran masu laifi wadanda a yanzu suke haifar da kalubalen tsaro ga wasu kasashen."

KU KARANTA: Ban taba saba wa doka ba a aikin gwamnati - Moghalu

“Mun hadu ne da kaddara daya don haka dole ne mu hada kai mu hada karfi da karfe mu kawar da wadannan mugayen mutane da ke addabar mutanen da ba su ji ba su gani ba.

Shugaba Buhari ya ce "Bari na yi amfani da wannan damar don nuna matukar damuwata ga gwamnati, mutanen Nijar da dangin wadanda abin ya shafa."

A wani labarin daban, 'Yan bindiga a daren ranar Asabar sun kai hari kauyen Kaya da ke Fatika a karamar hukumar Giwa ta Jihar Kaduna inda suka kashe mutum 15 sannan suka kona shaguna 11 da motocci biyar.

Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 8 na daren Asabar inda mazauna garin suka ce akwai yiwuwar harin ramuwar gayya ne game da harin da yan kauyen suka kai gidan shugaban yan fashi aka kashe yan uwansa uku.

Ibrahim Ahmed Fatika wadda ya ziyarci Kaya a safiyar ranar Lahadi ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa takwas cikin wadanda aka kashe yan Kaya ne yayin da sauran bakwai ciki har da direban trela baki ne da suka zo siyan takin kashin kaji.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel