Nijeriya ta fi yadda ta kasance muni a shekaru 6 - Jigo a jam'iyyar APC

Nijeriya ta fi yadda ta kasance muni a shekaru 6 - Jigo a jam'iyyar APC

- Wani jigo a jam'iyyar APC ta jihar Neja ya siffanta gwamnatin Buhari da gazawa wurin sauke hakkinta

- Jigon ya goyi bayan Bishop Mathew Kukah da ya caccaki mulkin Buhari a sakon Kirsimeti

- Ya kuma ja hankalin jama'a da su kula da maganganun Bishop din domin tunanin gyara a kasar

Yayin da sakon Bishop Matthew Kukah na Kirsimeti ke ci gaba da haifar da martani a tsakanin 'yan Najeriya, jigo a jam'iyyar All Progressive Congress (APC) kuma tsohon Kwamishinan Yada Labarai, Al'adu da yawon bude ido a jihar Neja, Mista Jonathan Vatsa, ya shawarci Gwamnatin Tarayya da matasan Arewa da su bar malamin a fuskanci magance matsalolin da ya gabatar, jaridar The Sun ta ruwaito.

Vatsa wanda shi ne kodinetan hulda da jama'a na Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a taken Minna "yaushe za mu karbi gaskiya" inda ya ce duk batutuwan da Kukah ya gabatar gaskiya ne.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Gombe zata dawo biyan ƙarancin albashi nan kusa

Ya ce abin takaici ne yadda wasu ‘’yan kwangila na siyasa ke zagon kasa kan abin da ya ce “gaskiya da kimanta gaskiya na halin da kasar ke ciki a yanzu.

“Kasar ta fi muni fiye da yadda take a shekaru shida da suka gabata. Babu wani abu da Bishop Kukah ya fada a cikin sakonsa na Kirsimeti wanda ba ya faruwa a kasar a yau.

Yanayin tsaro a kasar a yau ya fi kamari tun bayan samun 'yanci, duk kasar tana cikin kawanya daga masu aikata laifuka tare da mafi munin yanayi a arewa. Yin balaguro zuwa kowane yanki na arewa kamar zartar da hukuncin kisa ne a kan ka, ”in ji shi.

Ya yi zargin cewa rarrabuwar kawunan da ke tsakanin 'yan Nijeriya a karkashin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fi bayyana fiye da wanda ya auku na yakin basasa a shekaru 60 da suka gabata.

Najeriya ta fi yadda ta kasance muni a shekaru 6 - Jigo a jam'iyyar APC
Najeriya ta fi yadda ta kasance muni a shekaru 6 - Jigo a jam'iyyar APC Hoto: The Guardian
Asali: Facebook

Ya nuna nadamar cewa maimakon duba yadda Kukah ke bin kadin halin da kasar ke ciki da kuma kokarin samar da mafita a gare su, Gwamnatin Tarayya da masu mara mata baya suna ta guna-guni suna siyasantar da malamin Katolika din "sahihan abin lura."

Ya ce jihar Neja ta rasa zaman lafiya a cikin shekaru shida da suka gabata saboda ayyukan ‘yan fashi tare da gwamnati na kashe makuddan kudade wajen yakar matsalolin tsaro fiye da samar da kayayyakin more rayuwa.

KU KARANTA: Ban taba saba wa doka ba a aikin gwamnati - Moghalu

“Duk wani dan adam mai tunani mai kyau ya san cewa kasar na tafiya cikin rashin tsari da halin da ake ciki yanzu. Jihar Neja ta rasa sunan ta na alfarmar kasa zuwa gidan 'yan fashi. An mayar da gonaki filayen binne mutanen da 'yan fashi suka kashe, amma duk da haka ba mu son daukar suka. Dole ne a bar mutane su yada ra’ayoyinsu,” inji shi.

Vasta ya ce babban kalubalen da ke gaban gwamnatin Buhari shi ne yadda ta kasa yarda da suka na hakika, ta gyara kura-kuranta da ci gaba.

Ya ce baya ga kalubalen tsaro, yunwa da talauci sun mamaye kasar, yana mai cewa tsarin ciyar da matsakaicin dan Najeriya ya canza.

“Ko dai 1-0-0, 0-1-0, 1-0-1 ne ko kuma a wasu gidajen na 0-0-0. Fiye da 50% na gidajen Najeriya ba za su iya alfahari da abinci sau uku a rana ba,” inji shi.

A wani labarin, Yesufu ta lura cewa dan rajin kare hakkin dan adam, Omoyele Sowore, wanda aka kame a ranar 31 ga Disamba yayin wata zanga-zanga a Abuja, yana da damar yin zanga-zanga a kowace rana matuqar gwamnati na ci gaba da kasancewa "mai gazawa, mara ma'ana, da cin hanci da rashawa, Sahara Reporters ta ruwaito.

Wata mai rajin kare hakkin dan Adam kuma mai daukar nauyin kungiyar 'BringBackOurGirls Movement', Aisha Yesufu, ta caccaki gwamnatin da Shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta, tana mai cewa kasar ta kowa da kowa ce kuma ba wanda ya kamata a kame saboda zanga-zangar lumana.

A safiyar ranar Asabar, wani Babban Lauyan Najeriya, Mista Femi Falana, wanda shi ma lauya ne na Sowore, ya ce hukumomin ‘yan sanda sun fito karara sun ki amincewa da bukatar wanda yake karewa na beli.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel