Hotuna daga kasaitaccen bikin auren diyar kanin Aliko Dangote Aziza da Aminu

Hotuna daga kasaitaccen bikin auren diyar kanin Aliko Dangote Aziza da Aminu

- Aziza Dangote ta auri masoyinta, Aminu Waziri inda aka yi kasaitaccen biki na kece raini

- Auren kyakkyawar amaryar wacce ta kasance diyar kanin Aliko Dangote ya samu halartan manyan masu fada aji

- An gano Aliko, Saraki, Emefiele da wasu gwamnoni a hotunan bikin wanda tuni ya karade yanar gizo

An yi taro cikin walwala da annashuwa yayinda Aziza Dangote ta auri burin ranta Aminu Waziri a wani yanayi da za a iya kira da hadadden biki.

Kyakkyawar amaryar ta kasance diya ga Sani Dangote, wanda ya kasance mataimakin Shugaban kamfanonin Dangote tare da yayansa, Aliko Dangote.

KU KARANTA KUMA: Auren matashi dan Kano da Ba’amurkiya: Musulunci ya yarda da hakan, In ji Shehu Sani

Hotuna daga kasaitaccen bikin auren diyar kanin Aliko Dangote Aziza da Aminu
Hotuna daga kasaitaccen bikin auren diyar kanin Aliko Dangote Aziza da Aminu Hoto: @Instablog9ja
Asali: Twitter

Masoyinta, Aminu ya fito shar dashi cikin dakakken shadda dinkin babban riga yayinda Aziza ta fito cikin hadaddiyar dikin doguwar riga inda ta lullube kanta da mayafi shigen kayanta.

A hotunan bikin wanda tuni suka karade yanar gizo an gano Aliko, Saraki, Emefiele da wasu gwamnoni a masallacin da aka daura auren ma’auratan.

Kalli wallafar hotunan nasu a kasa:

KU KARANTA KUMA: Yadda jami’anmu suka kama wata babbar mota dankare da bindigogi 73 da harsasai 891 a Kebbi - Kwastam

Duk a lamarin makamancin wannan, tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya cika da farin ciki irin wanda kowani uba da ke alfahari da haihuwa yake shiga yayinda ya shaidi auren daya daga cikin yaransa maza.

Dan tsohon Shugaban kasar, Seun, ya angwance da amaryarsa, Deola Shonubi, a ranar Asabar, 12 ga watan Disamba, a gaban yan uwa da abon arziki.

A gano wasu jerin hotuna na ma’auratan a shafin Instagram din shahararriyar mai kwalliyar nan ta zamani, Banke Meshida, inda aka gano amaryar da mahaifiyarta suna shiri na wannan babban rana.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel