'Yan bindiga sun kashe mutum 15, sun kone motocci 5 da shaguna 11 a Kaduna (Hotuna)

'Yan bindiga sun kashe mutum 15, sun kone motocci 5 da shaguna 11 a Kaduna (Hotuna)

- Yan bindiga da ake zargin 'yan tawagar Filani ne sun kai hari kauyen Kaya da ke karamar hukumar Giwa a Kaduna sun kashe mutum 15

- Bayan kashe mutanen, sun kuma kone motocci biyar da shaguna guda 11 a harin da ake zargin na ramuwar gayya ne a daren ranar Asabar

- Mutane takwas cikin 15 da aka kashe yan asalin kauyen Kaya ne yayin da sauran kuma baki ne da suka zo siyan takin kashin kaji a Kaya

'Yan bindiga a daren ranar Asabar sun kai hari kauyen Kaya da ke Fatika a karamar hukumar Giwa ta Jihar Kaduna inda suka kashe mutum 15 sannan suka kona shaguna 11 da motocci biyar.

Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 8 na daren Asabar inda mazauna garin suka ce akwai yiwuwar harin ramuwar gayya ne game da harin da yan kauyen suka kai gidan shugaban yan fashi aka kashe yan uwansa uku.

Yan bindiga sun kashe mutum 15, sun kone motocci 5 da shagun 11 a Kaduna (Hotuna)
Yan bindiga sun kashe mutum 15, sun kone motocci 5 da shagun 11 a Kaduna (Hotuna). Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

Ibrahim Ahmed Fatika wadda ya ziyarci Kaya a safiyar ranar Lahadi ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa takwas cikin wadanda aka kashe yan Kaya ne yayin da sauran bakwai ciki har da direban trela baki ne da suka zo siyan takin kashin kaji.

DUBA WANNAN: Yadda za a kawo karshen 'yan bindiga a Arewa, Gwamna Bagudu

Ahmed ya bayyana cewa anyi jana'izar mutane takwas da abin ya ritsa da su a safiyar ranar Lahadi sannan an girke sojoji 10 a kauyen. Ya ce motocin da aka kona sun hada da Golf uku, da 406 da Bas yayinda an kuma kone shagon kafintoci.

'Yan bindiga sun kashe mutum 15, sun kone motocci 5 da shagun 11 a Kaduna (Hotuna)
'Yan bindiga sun kashe mutum 15, sun kone motocci 5 da shagun 11 a Kaduna (Hotuna). Hoto: daily_trust
Source: Twitter

Wani mazaunin kauyen, Abdu Saidu ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa harin na da alaka da kone gidan wani shugaban yan fashi mai suna Filani da kashe yan uwansa uku a ranar Asabar.

Ya ce ana zargin 'yan kungiyar Filani sun sace mutum biyar ciki har da wata da aka dab da daura wa aure a kauyen da ke makwabtaka da Kaura inda yace mutanen Kaura sun nemi taimako daga yan Kaya.

'Yan bindiga sun kashe mutum 15, sun kone motocci 5 da shagun 11 a Kaduna (Hotuna)
'Yan bindiga sun kashe mutum 15, sun kone motocci 5 da shagun 11 a Kaduna (Hotuna). Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

"An hanyarsu na kai taimako, daya daga cikin yan Kaya ya bace," in ji Saidu, ya kara da cewa: "Da suka gaza ceto wadanda aka sace, sunyi zargin yan kungiyar Filani ne suka kai harin don haka suka kone gidansa. Sun kuma sare danuwansa wadda daga bisani aka kai asibiti."

KU KRANTA: Mata mai sana'ar wankau ta gina gidan kanta, 'yan Najeriya sun taya ta murna

Saidu ya ce daga bisani sun gano gawar danuwansu a ranar Asabar da safe, daga nan suka tare dan uwan Filani da wasu yan uwansa biyu a hanyarsu na zuwa asibiti suka kashe su tare da kone gawarsu.

Rundunar 'yan sandan Kaduna da aka tuntube ta a ranar Lahadi ta ce a bata lokaci ta tattara bayanai kuma bata bada ba'asi ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel