Ban taba saba wa doka ba a aikin gwamnati - Moghalu

Ban taba saba wa doka ba a aikin gwamnati - Moghalu

- An nada Farfesa Kingsley Moghalu sarautar Nwewi ta "Ifek'ego Nnewi"

- Moghalu ya bayyana biyayyarsa ga aikin gwamnati da kiyaye dokoki

- Ya bayyana nada shi sarautar a matsayin bashi kwarin gwiwa na ci gaba da aiki tukuru

Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) kuma dan takarar shugaban kasa na Matasan Cigaban Party (YPP) a zaben 2019, Farfesa Kingsley Moghalu, an ba shi sarautar masarautar Nnewi ta "Ifek'ego Nnewi" (Mafi girma fiye da kudi) daga Igwe na Nnewi, HRH Dr Kenneth Orizu III, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun yi ruwan bama-bamai kan maboyar ‘yan ta’adda a Borno

Ban taba saba wa doka ba a aikin gwamnati - Moghalu
Ban taba saba wa doka ba a aikin gwamnati - Moghalu Credit: The Guardian
Source: UGC

Sarkin masarautar ne ya ba shi sarautar a wani kayataccen biki a Nnewi yayin bikin Igwe Orizu na shekara-shekara na Ofala karo na 57.

Tare da wannan sarautar, Moghalu yanzu mamba ne na shahararriyar kungiyar Manyan Sarakunan Nnewi, ɗaya daga cikin garuruwan kasuwanci mafi karfi a Najeriya.

A wani sanarwa da ya fitar jiya yace: “Sabon taken nawa sanarwa ce mai karfi na dabi’u a rayuwa. Mutunci ya fi kuɗi. A hidimtawa jama'a ga duniya da kasata, ban taba saba doka ba. Yana da mahimmanci abin da muke koya wa al'ummarmu da yadda ake tuna mu.

KU KARANTA: ‘Yan sanda sun cafke mutum 18 da ake zargi da tayar da tarzoma a Zamfara

“Sarautar ta zama mai mahimmanci saboda basaraken gargajiyar ya nuna godiya ga irin gudummawar da nake baiwa mahaifata. Wannan yana karfafa min gwiwa in ci gaba da bin turbar aiki, ”in ji shi.

A wani labarin, Babban bankin ƙasa CBN, ya fitar da zunzurutun kuɗi Naira biliyan N12.55 domin tallafawa masu kiwon kaji, a wani yunƙurin gwamnati na ƙara bunƙasa samar da ƙwai da naman kaji tare da samar da ayyukan yi a ƙasa baki ɗaya.

Bayanai daga bankin CBN sun nuna cewa an fitar da kuɗin ne tsakanin watannin ƙarshe na shekarar 2019 zuwa watan Nuwamba na shekarar 2020, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Daraktan gudanarwa a bangaren sha'anin kuɗi, Philip Yila Yusuf, ya tabbatar da haka inda ya ƙara da cewa ana kan tsare-tsaren bayar da rancen kuɗaɗen sakamakon ƙaruwar masu kiwon kajin da ake samu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel