Wata sabuwa: Mata da miji a kasar Indiya sun sanyawa jariran da suka haifa suna Corona da Covid

Wata sabuwa: Mata da miji a kasar Indiya sun sanyawa jariran da suka haifa suna Corona da Covid

- Wasu ma'aurata sun saka wa tagwayen da suka haifa yayin annobar coronavirus suna Corona da Covid

- Kamar yadda suka ce, duk da cewa sunayen na kwayoyin cuta ne, amma kwayoyin cutar basu son kazanta kuma sun saka mutane da yawa fara tsafta

- Mahaifiyar jariran mai shekaru 27 ta bayyana cewa tana matukar farinciki kuma tagwayen na bayyana nasara ne a yayin da matsi ya yawaita garesu

Wasu ma'aurata sun saka wa tagwayen da suka haifa suna 'Corona' da 'Covid' duk da tashin hankalin da annobar ta haifar a duniya.

Kalmomi biyu na 'Corona' da 'Covid' an samo su ne daga kwayar cutar coronavirus, mummunar cutar da ta fara barkewa daga garin Wuhan a kasar China.

Wata sabuwa: Mata da miji a kasar Indiya sun sanyawa jariran da suka haifa suna Corona da Covid
Wata sabuwa: Mata da miji a kasar Indiya sun sanyawa jariran da suka haifa suna Corona da Covid
Asali: Facebook

Ma'auratan 'yan asalin Chhattisgarh sun haifa tagwayen ne a yayin da coronavirus ta barke. Hakan ne kuwa yasa suka rada musu suna 'Corona' da 'Covid'. Sun ce wannan alamar nasara ce a yayin tsananin rayuwa.

Kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito, ma'auratan sun ce sunayen za su tunatar musu da duk tsananin da suka fuskanta yayin annobar.

"Ubangiji ya albarkacemu da tagwaye, mace da namiji a sa'o'in farko na ranar 27 ga watan Maris. Mun saka musu Covid (namijin) da Corona (Macen)," Preeti Verma mai shekaru 27 wacce ita ce mahaifiyar jariran ta bayyana.

KU KARANTA: Mutumin da ya kamu da cutar Coronavirus ya tofawa wani yawu a fuska kafin ya fadi ya mutu a wajen

"An haifesu ne bayan fuskantar matsin rayuwa sakamakon annobar coronavirus, don haka ni da mijina muka yanke shawarar saka musu suna mai tarihi.

"Gaskiya kwayar cutar na da hatsari kuma tana babbar barazana ga rayukan jama'a. Kwayar cutar ba ta zama wajen kazanta don haka ta sauyawa mutane da yawa halayyarsu. Hakan yasa muka yi tunanin saka sunayen," ta ce, yayin da take bada dalilan saka sunayen.

"A lokacin da ma'aikatan asibitin suka fara kiransu da Corona da Covid, sai muka yanke shawarar saka musu sunan annobar," tace.

Jami'in hulda da jama'a na asibitin da aka haifa tagwayen, Shubhra Singh ya ce, mahaifiyar da tagwayen an sallamesu babu dadewa sannan suna cikin koshin lafiya.

"A cikin mintuna 45 bayan isowarsu aka haifesu cike da koshin lafiya," ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel