Buhari zai rattafa hannu kan kasafin kudin 2021 yau

Buhari zai rattafa hannu kan kasafin kudin 2021 yau

Shugaba Muhammadu Buhari yau, Alhamis, 31 ga Disamba, 2020, zai rattafa hannu kan kasafin kudin 2021 da majalisar dokokin ta amince da shi makon da ya gabata.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya tabbatar da hakan, rahoton Daily Trust.

Wadanda ake kyautata zaton za su halarci taron sune; mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; Kakakin majalisar wakilai. Femi Gbajabiamila; shugabannin majalisa, da kuma shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa da na wakilai.

Mambobin majalisar zartaswa FEC da ake sa ran zasu halarta sun hada da Ministar kudi, Hajiya Zainab Ahmed; karamin ministan kasafin kudi, Clement Agba; gwamnan CBN, Godwin Emefiele; da dirakta janar na ofishin kasafin kudi, Ben Akabueze, dss.

Hadimin Buhari kan lamuran majalisar dattawa, Sanata Babajide Omoworare, da hadimin na bangaren majalisar wakilai, Umar El Yakub, ne zasu gabatar da daftarin kasafin kudin ga Buhari.

Amma, dubi ga irin yanayin Korona da ake ciki, taron na iya gudana ta yanar gizo.

Buhari zai rattafa hannu kan kasafin kudin 2021 yau
Buhari zai rattafa hannu kan kasafin kudin 2021 yau Hoto: Presidency
Source: Twitter

A ranar Litinin, fadar shugaban kasa ta karbi daftarin kasafin kudin daga wajen yan majalisa.

A ka'ida idan yan majalisar dokoki suka amince da kasafin kudin kuma suka kai fadar shugaban kasa, za'a gayyaci ministoci su duba.

Manufar haka shine tabbatar da cewa irin sauye-sauyen da yan majalisan suka yiwa kasafin kudin.

A ranar 21 ga wata, majalisar dattawa Najeriya ta amince da kasafin kudin N13.588 tiriliyan na shekarar 2021 da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar watanni biyu baya.

Hakan ya biyo bayan kammala aikin da kwamitin lissafe-lissafen kasafin kudi da tayi kan kasafin kudin.

Shugaban kwamitin, Sanata Barau Jibrin, ya gabatar da daftarin kasafin kudin a ranar Litinin, 21 ga watan Disamba, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel