Jihohi 10 da suka fi dogara da kasafin wata-wata na gwamnatin tarayya

Jihohi 10 da suka fi dogara da kasafin wata-wata na gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya, jihohi 36 na kasar nan da kananan hukumomi fiye da 700 suna raba kudin shigar da aka samu daga danyen mai duk wata.

Duk matakan gwamnati suna bukatar amfani da kudi da kuma harajin cikin gida don kula da bukatun su.

Kwamitin rarraba kudi na gwamnatin tarayya (FAAC) ne ya ke rarraba kudin. Kuma an fitar da jihohi goma da suka fi dogara da kasafin kudin.

Jihohi 10 da suka fi dogara da kasafin wata-wata na gwamnatin tarayya
Jihohi 10 da suka fi dogara da kasafin wata-wata na gwamnatin tarayya. Hoto: Femi Adesina
Asali: Twitter

A daya bangaren, wasu jihohin ba su dogara da kason ba saboda yanayin tattalin arziki da kuma yadda suke tara kudaden shiga

DUBA WANNAN: Hatsarin mota ya halaka mutane 40 a Adamawa, FRSC

A daya hannun, wasu jihohi zai wahala sukai labari ba tare da wancan kaso ba, saboda karancin kudaden shiga.

Legit.ng a wannan rubutu ta ruwaito jihohi 10 da suka fi dogara da kasafin wata wata na gwamnatin tarayya daga rahoton ma'aikatar kididdiga (National Bureau of Statistics NBS).

Ga jerin jihohin nan a kasa:

1. Bayelsa (89.6%)

2. Borno (88.3%)

3. Katsina (88.2%)

4. Kebbi (87.8%)

5. Taraba (87.7%)

6. Yobe (85.9%)

7. Gombe (85.8%)

8. Ebonyi (85.7%)

9. Akwa Ibom (84.2%)

10. Adamawa (83.3%)

KU KARANTA: Zahra Buhari ta taya mijinta murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kalaman soyayya

A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shugaban hukumar daukan ma'aikata, Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungu daga mukaminsa.

Sanarwar saukewar na kunshe ne cikin wata wallafa da babban mataimakin shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta ce Buhari ya umurci karamin ministan Kwadago da Ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ya nada shugaban riko daga cikin manyan direktocin hukumar don maye gurbin Argungu a yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel