‘Yan sanda sun kame wadanda ake zargi da yin garkuwa da Bishop din Katolika na Owerri
- 'Yan sanda sun yi nasar cafke masu garkuwa da mutane a jahar Imo
- An samu nasarar ceto Bishop Moses Chikwe da wasu mutane a afkawa masu garkuwa da mutanen da akayi
- 'Yan sanda sun bayyana neman goyon bayan jama'a domin ci gaba da samun nasara akan masu aikata laifuka
Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Imo ta ce ta cafke wasu mutane da ke da alaqa da sace mataimakin Bishop na Katolika Archdiocese na Owerri, Moses Chikwe.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar, Orlando Ikeokwu, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Owerri, Sahara Reporters ta ruwaito.
A cewar jaridar Vanguard, jami’in ya ambaci cewa daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su har da direban Bishop Chikwe da kuma wata mata mai shekaru 33, Chioma Stephanie Ekwedike, wacce aka sace a gaban gidanta, a Imo Housing Estate Umuguma, karamar hukumar Owerri ta yamma.
KU KARANTA: Jami'an yan sanda sun dakile harin yan bindiga, sun ceto wanda aka sace
‘Yan sanda sun ci gaba da cewa an kubutar da bishop din tare da wasu daga cikin wani daji mai kauri, tsakanin Awara a karamar hukumar Ohaji / Egbema ta jihar Imo da rafin Omuku da ke jihar Ribas, karkashin sashin yaki da satar mutane.
Sun lura cewa yayin aikin ceton, wasu daga cikin gungun masu garkuwan sun gudu kuma rundunar ta kara himma don cafke su.
‘Yan sanda sun ba da labarin cewa, “An samu nasarar ceto mataimakin Bishop na Katolika Archdiocese na Owerri, Bishop Moses Chikwe, ba tare da jin rauni ba a sakamakon wani samame da rundunar ‘yan sanda da ke karkashin sashin yaki da satar mutane suka kai.
“Ku tuna cewa a ranar 27/12/2020, an sace mataimakin Bishop na Archdiocese din tare da direbansa, kuma‘ yan bangan sun ci gaba da yin garkuwa da Chioma Stephenie Ekwedike (F), mai shekaru 33, a Imo Housing Estate Umuguma, a gidanta dake karamar hukumar Owerri ta yamma.
"Bisa ga abin da ke sama, shugaba kuma jami'in da ke kula da rundunar 'yan sanda ta jihar, wanda ya kasance sabon mukamin AIG Isaac Akinmoyede, ya yi amfani da dukkan kungiyoyin dabarun da ke cikin rundunar, kuma ya umarce su da su ceci bishop din da sauran su, kuma su kama' yan fashin da ke da alhakin aikin.
“Yin aiki da wannan umarnin, hadadden rukunin dukkanin kungiyoyin dabarun a ranar 31 ga watan Disamba, 2020 sun afkawa Awara, karamar hukumar Ohaji / Egbema da rafin Omuku. Mutane kaɗan da ke da alaƙa da aikata laifin / masu laifi an kama su, kuma an gano wasu abubuwa da mallakarsu laifi ne.
"Kama wadanda ake zargin da sauran ayyukan hadin gwiwar da rundunar ta yi ya sa masu garkuwar suka yi watsi da wadanda abin ya rutsa da su, lamarin da ya kai ga kubutar da bishop din tare da wasu mutane biyu da lamarin ya rutsa da su ba tare da an biya su kudin fansa ba. Ana ci gaba da kokarin kame mambobin kungiyar masu garkuwa da mutane.”
Rundunar 'yan sandan Imo ta ci gaba da cewa, "Rundunar na kuma yaba wa jama'a da kuma al'ummar Kirista saboda nutsuwa (da aka samu) a lokacin wannan wahala da kuma kwarin gwiwar da' yan sanda na Najeriya suka samu na magance wannan laifi.
KU KARANTA: Umakhihe yayi alƙawarin samar da tsari don saurin samar da wadatar abinci
"Amma, muna so mu tabbatarwa da kowa cewa rundunar zata ci gaba da kare dukkan 'yan jihar masu kiyaye doka.
“Ana tunatar da jama’a cewa duk abin da ya faru a yankin su dole ne a hanzarta kai rahoto ga‘ yan sanda, musamman abubuwan da ke faruwa na mummunan yanayi ko munanan laifuka.
"Rundunar tana kuma kira da a samu bayanai daga jama'a game da aikata laifuka da laifuka a yankinsu domin baiwa 'yan sanda damar daukar mataki cikin hanzari."
A wani labarin, Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya bukaci al’umman kasar da su koyi darasi daga matsaloli, riba da rashin da aka yi a shekarar 2020.
Jonathan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 1 ga watan Janairu, a sakonsa na sabuwar shekara zuwa ga yan Najeriya ta shafin Twitter.
Tsohon Shugaban kasar ya ce 2020 ta kasance shekara mai tattare da kalubale ga gidaje da iyalai da dama saboda annobar korona.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng