Sakon sabuwar shekara: Jonathan ya bukaci yan Najeriya da su rungumi adalci da zaman lafiya

Sakon sabuwar shekara: Jonathan ya bukaci yan Najeriya da su rungumi adalci da zaman lafiya

- Goodlucck Jonathan ya bayar da bayanai kan yadda yan Najeriya za su iya rayuwa mai amfani a sabuwar shekara

- Tsohon shugaban kasar ya gano wasu koma baya da suka afku a kasar a 2020

- Jonathan ya bayyana dalilin da yasa bai kamata al’umman kasar su bari matsalolin baya ya shafi makomarsu na gaba ba

Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya bukaci al’umman kasar da su koyi darasi daga matsaloli, riba da rashin da aka yi a shekarar 2020.

Jonathan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 1 ga watan Janairu, a sakonsa na sabuwar shekara zuwa ga yan Najeriya ta shafin Twitter.

Tsohon Shugaban kasar ya ce 2020 ta kasance shekara mai tattare da kalubale ga gidaje da iyalai da dama saboda annobar korona.

Sakon sabuwar shekara: Jonathan ya bukaci yan Najeriya da su rungumi adalci da zaman lafiya
Sakon sabuwar shekara: Jonathan ya bukaci yan Najeriya da su rungumi adalci da zaman lafiya Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Facebook

KU KARANTA KUMA: Buhari ya kadu matuka da rasuwar Iyan Zazzau da Taliban Zazzau

Ya ce baya ga annobar, Najeriya ta kuma yi fama da zanga-zangar EndSARS da tabarbarewar al’ada, tattalin arziki, harkoki da rayuwa al’umma.

Jonathan ya bayyana cewa duk da koma bayan, ya kamata yan Najeriya su koyi darasi daga matsalolin baya.

Ya shawarci al’umman kasar da su ba da muhimmanci ga halayyar da ke nuni ga adalci da zaman lafiya a tsarin Najeriya.

Jonathan ya yaba ma dukkanin yan Najeriya a kan karfin gwiwar da suka nuna a yayinda ake tsaka da fama da matsaloli.

Ya kuma yi ta’aziyya ga iyalan da suka rasa masoyansu sakamakon korona da sauran cututtuka da matsaloli a shekarar 2020.

KU KARANTA KUMA: Prophet Nigel Gaisie ya ce Osinbajo zai zama shugaban kasar Nigeria

A wani labarin, a yayinda Najeriya ke tsaka da fuskantar matsaloli, tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya bukaci yan Najeriya da su ci gaba da hakuri da gwamnati.

Babangida wanda ya bayyana hakan a yayinda yake jawabi a wata hira da Channels Television ya bukaci yan kasa da su zamo masu hakuri.

A cewar tsohon shugaban kasar, duk abunda yayi farko zai yi karshe. Ya ci gaba da bayana cewa da zaran yan Najeriya sun zage damtse wajen aiki don cimma manufa, kowa zai ji dadi a 2021.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel