Prophet Nigel Gaisie ya ce Osinbajo zai zama shugaban kasar Nigeria

Prophet Nigel Gaisie ya ce Osinbajo zai zama shugaban kasar Nigeria

- Wani Shugaban addini a kasar Ghana, Prophet Nigel Gaisiehas ya yi wasu hasashe game da abubuwan da yake ganin za su faru a nan gaba

- Daya daga cikin hasashen ya kasance game da makomar siyasar mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo

- Osinbajo bai saki kowani jawabi game da shirinsa bayan barin kujerarsa a 2023

Wani fasto mazaunin kasar Ghana, Prophet Nigel Gaisie, ya yi hasashen cewa mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo zai zama Shugaban kasar Najeriya.

BBC ta ruwaito cewa faston, wanda ya kasance Shugaban cocin Prophetic Hill Chapel Prophet ya yi hasashen a lokacin wa’azinsa na shiga 2021.

KU KARANTA KUMA: Farin cikin sabuwar shekara yayinda El-Rufai ya ji kan wasu fursunoni 12, ya yi umurnin sakinsu

Prophet Nigel Gaisie ya ce Osinbajo zai zama shugaban kasar Nigeria
Prophet Nigel Gaisie ya ce Osinbajo zai zama shugaban kasar Nigeria Hoto Laolu Akande
Source: Facebook

Ya ce:

“Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo zai zama shugaban kasa.”

Sai dai Gaisie, bai yi bayani kai tsaye ba kan ko hasashensa kan Osinbajo zai zo ne bayan gwamnatin Buhari ko kuma wani lokaci a nan gaba.

Faston ya kuma ce koda dai duniya za ta samu zaman lafiya, za a aiwatar da wani harin ta’addanci a kasar Amurka.

Ya kuma yi hasashen cewa wani shahararren mai wa’azi zai mutu a 2021.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa ba zan bar PDP ba, Gwamna Ikpeazu ya magantu

A wani labari, a yayinda Najeriya ke tsaka da fuskantar matsaloli, tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya bukaci yan Najeriya da su ci gaba da hakuri da gwamnati.

Babangida wanda ya bayyana hakan a yayinda yake jawabi a wata hira da Channels Television ya bukaci yan kasa da su zamo masu hakuri.

A cewar tsohon shugaban kasar, duk abunda yayi farko zai yi karshe. Ya ci gaba da bayana cewa da zaran yan Najeriya sun zage damtse wajen aiki don cimma manufa, kowa zai ji dadi a 2021.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel