Za mu kunyatta 'yan ta'adda a 2021, in ji Buratai

Za mu kunyatta 'yan ta'adda a 2021, in ji Buratai

- Rundunar sojojin Najeriya ta yi wa 'yan ta'adda da ke kai hare-hare a garuruwa albishir da azaba mai radadi a shekarar 2021

- Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Tukur Buratai, ya ce 'yan ta'adda za su kare shekarar nan cikin kunya

- Buratai ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya ke yi wa dakarun sojojin kasar jawabi a Jihar Borno da ke Arewa maso Gabas

Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Tukur Buratai, ya ce rundunar sojoji zata kunyatta 'yan Boko Haram da Kungiyar States for West African Province (ISWAP) a shekarar 2021.

Buratai ya bada wannan tabbacin ne a wurin wani taro da aka yi a garinsu da ke karamar hukumar Biu da ke Jihar Borno kamar yadda Daily Sun ta ruwaito.

2021: Za mu kunyatta 'yan ta'adda, in ji Buratai
2021: Za mu kunyatta 'yan ta'adda, in ji Buratai. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Abinda yasa na bari wani daban ya yi min ciki a gidan mijina, matar aure

Ya ce:

"Na yi imamin cewa abubuwa za su sauya a shekarar 2021, za a samu muhimmin banbanci ta yadda abubuwa suka kasance a shekarar 2020.
"Ina son ku dauki shi a matsayin kallubale da aiki da ya zama dole a yi kuma mu ne za muyi aikin domin 'yan Najeriya sun yi yarda da mu kuma sunyi imanin cewa za mu iya aiwatar da aikin.
"Ku shiga wannan sabon shekarar da niyyar cewa za mu iya yin abinda ya fi wanda muka yi a baya domin magance matsalar tsaro a kasar mu."

KU KARANTA: Jaruma Didi Ekanem ta shawarci 'yan mata su rika soyayya da samari talakawa a 2021

Wasu 'yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu kan kalaman na Buratai a kafafen sada zumunta.

Olukayode Rotimi a Facebook ya rubuta:

"Ba ku kunyata yan ta'addan a 2020 ba, sai a 2021 ne zaku kunyata su? Wannan na nuna baka cancanta zama babban hafsan sojoji ba, abin kunya ga sojojin mu."

Joshua Ebiloma ya rubuta:

"Mun gaji da irin wannan cika bakin, kawai ku aiwatar da shi."

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel