Jaruma Didi Ekanem ta shawarci 'yan mata su rika soyayya da samari talakawa a 2021

Jaruma Didi Ekanem ta shawarci 'yan mata su rika soyayya da samari talakawa a 2021

- Jaruma Didi Ekanem ya wallafa wasu shawarwari ga yan mata a shafin sada zumanta

- Jarumar ta gargadi yan mata da su daina soyayya da samarin kawayen su

- Ekanem ta shaida cewa duk da kudi yana da amfani, bai kamata ya zama kashin bayan kowace alaka ba

Jarumar fina finan Nollywood Didi Ekanem ta janyo cecekuce a kafar sada zumanta bayan ta shawarci yan mata kan hanyoyin da su bi a soyayya cikin shekara mai kamawa ta 2021 da ta rage kwanaki kadan.

Jarumar, a shafinta na instagram ta fara da nuna cewa bai kamata a takurawa mace akan irin namjin da ta zaba a matsayin abokin rayuwa ba.

Jaruma Didi Ekanem ta shawarci talakawa su rika neman mata irinsu
Jaruma Didi Ekanem ta shawarci talakawa su rika neman mata irinsu. Hoto: @didiekanem
Source: Instagram

DUBA WANNAN: Zamfara: 'Yan bindiga sun kashe dillalin da shanu saboda yaki siyan shanun sata

Ekanem ta buga misali da yadda iyaye a baya suke zabar mazajen aure ba tare da duba nakasun rashin kudi ba.

Ta sake bayyana cewa yan matan da basu yi dacen samun mazan da zasu dinga kashe musu kudade ba, kada su dinga sawa sauran mata suna jin sauran maza haka suke.

KU KARANTA: Kotu ta tura wani gidan yari saboda yi wa Gwamna Badaru ƙazafi a Facebook

"Idan da iyayen mu mata basu auri talakawan iyayen mu maza ba, to da yanzu ba a same mu ba. Idan kinyi sa'a kin samu namiji mai kula da ke, to kada ki sanya wasu matan suji su basu da sa'a saboda kaddarar kowa akwai bambanci."

Jarumar ta ce duk da kudi suna da amfani, bai kamata ya zama kashin bayan alakar arziki ba. Ekanem tayi misali da yadda yan mata suka janyo wasu mazan fadawa laifuka duk da sunan neman kudi.

"Kudi yana da amfani amma bai kamata ya zama kashin bayan kyakkyawar alaka ba. Ku daina kiran maza talakawa. In suka zama yan fashi yanzu, ku za ku yi korafi. Idan suka zama barayi a yanar gizo, za kuyi Allah wadai, bazan iya auren barawo ba, amma kuna kiran su talakawa."

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yiwa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.

Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.

Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel