Atiku Abubakar ya ce dole PDP ta hade don cimma nasara a 2023
- Tuni jam’iyyar PDP ta fara shirye-shirye don tabbatar da samun kuri’u mafi rinjaye a zabn 2023
- Jam’iyyar ta gudanar da wani taro a jihar Ebonyi don ci gaba da karfafa hadin kai a tsakanin mambobinta
- Yan Najeriya za su yi zabe a 2023 domin zabar sabon Shugaban kasa da zai yi jagoranci a shekaru hudu masu zuwa
Tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayar da bayani kan yadda jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) za ta iya yin nasara a zaben 2023.
Dan siyasan wanda yayi takarar kujerar Shugaban kasa karkashin jam’iyyar ya ce doe PDP ta hade domin samun nasara a zaben 2023, Vanguard ta ruwaito.
Ya bayar da shawarar a ranar Talata, 29 ga watan Disamba, a wani taron siyasa a karamar hukumar Afikpo ta kudu da ke yankin Ebonyi ta kudu.
KU KARANTA KUMA: Iyalan dan Najeriya da aka yankewa hukuncin kisa a Saudiyya sun roki FG da ta ceto shi
Tsohon mataimakin Shugaban kasar ya ce:
“A matsayinmu na jam’iyya domin ci gaba da samun nasara a zabukanmu na gaba ya zama dole PDP ta ci gaba da kasancewa cikin zaman lafiya da hadin kai a dukkan mataki, domin hadin kai shine mabudin nasara a zabenmu, muna da yawan da ake bukata, mutane, karfi, dabaru da shugabanni a jihar Ebonyi.”
A cewar jaridar Leadership, Atiku ya ce PDP na kara karfi a jihat Ebonyi. Ya bukaci mambobin jam’iyyar a jihar da su ci gaba da jajircewa ta fuskacin matsaloli.
KU KARANTA KUMA: Nigeria: Abubuwa 3 da ba a taba tunanin za su afku a 2020 ba
A wani labari, babbar kungiyar zamantakewa da siyasa, kungiyar tuntuba ta arewa (ACF), ta kwarmata cewa yanzu da rakuma ake amfani wajen shigo da makamai yankin arewa.
ACF ta bayyana cewa ana amfani da Rakuma wajen safarar manyan bindigu na RPG da bindigun harbo jirgin sama zuwa Nigeria ta kan iyakokin da ke arewa.
Cif Audu Ogbeh, shugaban ACF, shine ya bayyana hakan a cikin wani jawabi mai dauke da sa hannunsa wanda ya fitar ranar Alhamis.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng