Kotun daukaka kara ta fatattaki shugaban kwamitin rikon kwaryan APC a Ribas

Kotun daukaka kara ta fatattaki shugaban kwamitin rikon kwaryan APC a Ribas

- Wani bangare na jam'iyyar APC ya yi martani ga hukuncin kotun daukaka kara wanda ta kori shugaban kwamitin rikon kwaryanta a Ribas

- Wani jigo na jam'iyyar, Isaac Ogbula ya yi magana a kan dalilin da yasa suka karba wannan hukuncin da hannu bibbiyu

- Dan siyasan ya zargi wasu mutane da aikin zagon kasa ga ra'ayoyin jam'iyyar a jihar Ribas

Kotun daukaka kara ta fatattaki Igo Aguma a matsayin shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC a jihar Ribas.

Wani bangaren APC na jihar wanda ke samun shugabancin Isaac Ogbobula ya kwatanta hukuncin kotun daukaka karan da abun jinjina, The Nation ta ruwaito.

Ogbobula a ranar Talata, 29 ga watan Disamba ya ce, wannan hukuncin ya kawo saiti tare da tsarki a jam''iyyar.

Kamar yadda jigon jam'iyyar yace: "Muna jinjina ga hukuncin kotun daukaka kara a kan ingantaccen hukuncinta na ranar Talata, wanda ta tabbatar da saiti tare da aike muhimmin sako ga kotunan kasa da ita da su kiyaye shiga lamurran cikin gida na jam'iyyun siyasa."

KU KARANTA: Bidiyon mayakan ISWAP suna kashe wasu 'yan Najeriya 5 ya gigita jama'a

Kotun daukaka kara ta fatattaki shugaban kwamitin rikon kwaryan APC a Ribas
Kotun daukaka kara ta fatattaki shugaban kwamitin rikon kwaryan APC a Ribas. Hoto daga @Bunimedia
Asali: Twitter

Ogbobula ya ce hukuncin kotun ya bai wa jam'iyyar damar cigaba.

Ya yi kira ga jajirtattun mambobin jam'iyyar APC da su ceto jam'iyyar daga hannun 'yan siyasa 'yan gangan.

Kamar yadda yace: "Dole ne mu tuhumi tsare-tsare, shirye-shirye da kuma duk ayyukan jihar nan da kuma yadda abubuwa ke kasancewa."

KU KARANTA: 2023: Afenifere ta bayyana matakin da ta dauka idan Jonathan ya fito takara

A wani labari na daban, jigon jam'iyyar APC, Sanata Abba Ali, ya yi martani a kan kara lalacewar tsaron kasar nan. Ya ce shugaan kasa Muhammadu Buhari ya gaji wadannan matsalolin ne daga jam'iyyar PDP.

Ali, wanda ya yi magana daga Katsina, ya bayyana hakan a ranar Laraba ta wata hirar wayar tafi da gidanka da yayi da gidan talabijin na Chhannels TV a shirin siyasarmu a yau.

"Rashin tsaron da ke addabar kasar nan ba tun yanzu yake ba. An gaje shi ne daga jam'iyyar PDP tun lokacin da suke mulki," mamba a kwamitin rikon kwarya na APC yace."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel