Nigeria za ta tsinci kanta dumu-dumu a cikin nasara da wadata, In ji Maharaji

Nigeria za ta tsinci kanta dumu-dumu a cikin nasara da wadata, In ji Maharaji

- Najeriya za ta samu tarin wadata a bangarori da dama a shekarar 2021 da za a shiga

- Wannan shine wahayin da Satguru Maharaji na One Love Family ya saki

- Maharaji ya kuma yi hasashen ganin karshen matsalolin rashin tsaro da ya addabi Najeriya

Satguru Maharaji Shugaban gidauniyar One Love Family ya saki wahayi mai dadin ji game da Najeriya, tattalin arzikinta da gwamnati gabannin shekarar 2021.

A cewar Maharaji, kasar za ta tsinci kanta a yanayin ci gaba da wadata ta kowani bangare na rayuwarta, musamman ta bangaren tattalin arziki, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Baya ga kaddamar da cewar kasar za ta daidaita ta fuskacin tattalin arziki a wannan shekarar, matsafin ya yi hasashen cewa lamarin rashin tsaro da kasar ke ciki a yanzu zai zama tarihi kwanan nan.

Nigeria za ta tsinci kanta dumu-dumu a cikin nasara da wadata, In ji Maharaji
Nigeria za ta tsinci kanta dumu-dumu a cikin nasara da wadata, In ji Maharaji Hoto: Vanguard
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Kasar New Zealand ta yi bankwana da 2020, tana bikin shiga shekarar 2021

Sai dai kuma, don cimma haka, ya ba gwamnatin tarayya shawarar samar da tsarin kula da farashin abubuwa.

A bangaren siyasa, ya bayyana cewa a ci gaba da tsarin nan da baya rubuce a kundin tsarin mulki inda arewa ke mulkin shekaru takwas sannan ta mika wa kudu mulki.

Maharaji ya ce:

“Ba wai ina bayar da shawarar cewa dole ne sai wata kabila ta samar da Shugaban kasa a 2023 bane, amma na yarda cewa ya kamata mu sami shugaba da ke so da damuwa da al’umma.

“A ci gaba da yarjejeniyar da baya rubuce inda arewa ke mulki na shekaru takwas annan a mika mulki ga kudu.”

KU KARANTA KUMA: Manyan ayyuka 9 da ma'aikatar Pantami ta gudanar a shekarar 2020

A wani labari na daban, wani mamba a kungiyar dattawan Arewa ta ACF ya yanke kauna kan shirin gwamnatin tarayya na magance matsalar rashin tsaro a Najeriya.

Kakakin kungiyar, Emmanuel Waye, ya ce ya yanke kauna da gwamnatin Shugaban kasa Buhari wajen kawo karshen matsalar da ya addabi kasar.

Waye ya bayyana cewa ba zai iya tafiya zuwa jiharsa ba, Taraba, saboda tsoro, inda ya kara da cewa hakan yake a tsakanin yan arewa da dama.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng