Dole Jam’iyyar PDP ta hada-kai domin samun nasara a zaben gaba inji Atiku

Dole Jam’iyyar PDP ta hada-kai domin samun nasara a zaben gaba inji Atiku

- Atiku Abubakar ya yi jawabi wajen wani gangamin PDP a jihar Ebonyi

- Tsohon mataimakin shugaban Najeriyar ya yi kiran a samu hadin-kai

- Atiku ya caccaki masu sauyin-sheka daga PDP, su koma jam’iyyar APC

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce sai jam’iyyar PDP ta hada kan gidanta kafin ta iya samun nasarori a zabukan 2023.

Jaridar Vanguard ta rahoto Alhaji Atiku Abubakar ya ce sai ‘Dan siyasa maras basira ne zai sauya-sheka daga PDP ya koma APC a marrar nan.

Wazirin Adamawa ya yi wannan bayani ne a wajen wani gangami da jagoran PDP, Dr. Onuoha Nnachi ya shirya a garin Afikpo, jihar Ebonyi.

“Idan mu na so mu samu nasara a zaben da za ayi nan gaba, dole PDP ta zauna lafiya, cikin hadin-kai a duka matakai, shi ne hanyar lashe zabe.”

KU KARANTA: Abin da ya sa Sanatan Adamawa ya koma APC

Atiku Abubakar ya cigaba da cewa: “Mu na da kuri’u, da jama’a dabaru da shugabanni a Ebonyi.”

Ya ce: “Danyen aikin da gwamna ya yi abin takaici ne, dama siyasa ta gaji haka, don haka dole mu jajirce, PDP ta na da matukar karfi a jihar Ebonyi.”

Atiku ya ce nan gaba gwamnan Ebonyi David Umahi zai fadawa Duniya ainihin dalilin barinsa PDP. Oladimeji Fabiyi ne ya karanto jawabin na sa.

'Yan siyasar da su ka halarci wannan taro sun hada da: Cif Ali Odefa, Sanata Michael Ama Nnachi, Hon. Iduma Igwariwey, da Hon. Fred Udeogu.

KU KARANTA: Atiku ya kaddamar masu yi masa yakin neman zabe

Dole Jam’iyyar PDP ta hada-kai domin samun nasara a zaben gaba inji Atiku
Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar Hoto: Legit/legit.ng
Asali: UGC

Gangamin ya kuma samu halartar irinsu Sylvester Ogbagba, Julius Ama Orji, Fidelis Nwankwo, Ajim Best, Emmanuel Kanodu, da kuma Abiam Onyike.

A ranar Laraba ne Sanata Elisha Abbo ya jadada cewa zai yi takarar gwamnan jihar Adamawa a 2023 bayan ya sauya-sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki

Sanatan mai wakiltan Adamawa ta Arewa ya ce ya fice daga PDP ne saboda jam'iyyar ta mutu

Elisha Abbo ya bayyana cewa ba rikicinsa da Gwamna Amadu Fintiri bane yasa ya fice daga PDP. Abbo ya yi wannan jawabi ne a mahaifar Atiku Abubakar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng