Mu na da matukar karancin wadanda su ka san kan aiki a 1956 inji Tanko Yakasai
- Tanko Yakasai ya bayyana abin da ya hana Arewa goyon bayan ‘yancin-kai a 1956
- Dattijon ya ce a lokacin da aka kawo maganar, babu masu Digiri a bangaren Arewa
- A dalilin haka manyan yankin suka nemi a dakatar da maganar sai Arewa ta shirya
Fitaccen dattijon nan, Tanko Yakasai, ya ce yankin Arewa bai amince da maganar bada ‘yanci a 1956 ba ne saboda karancin ma’aikata a lokacin.
Alhaji Tanko Yakasai ya ce sa’ilin da wasu ke neman a ba Najeriya ‘yancin kai a 1956, babu isassun ‘Yan Arewa da za su iya rike wuraren aiki.
Tanko Yakasai wanda ya ke siyasa tun a jamhuriya ta farko, kuma ya rike mukami a gwamnatin Shehu Shagari ya bayyana abin da ya faru a lokacin.
Dattijon ya shaidawa jaridar Punch cewa a 1953 ne Cif Anthony Enahoro na jam’iyyar Action Group ya kawo maganar a ba Najeriya ‘yancin kai.
KU KARANTA: Kasafin kudin 2021 ya shiga cikin dokar kasa
Ya ce: “Wani ‘dan majalisar Arewa ya yi wa maganar kwaskwarima, ya bukaci a canza shekarar 1956 da ake hari zuwa duk lokacin da abin zai yiwu.”
Kaf yankin Arewacin Najeriya, mutum guda ake da shi wanda ya halarci jami’a, ya samu Digiri. Yakasai ya ce wannan mutum shi ne Dr. R. A. B. Dikko.
“Saboda a 1953, gaba daya Arewa mai 75% na arzikin kasa da 55% na al’ummar Najeriya, ta na da mai digiri daya ne kawai, Dr. R.A.B Dikko.” Inji Yakasai.
A daidai wannan lokaci kuma akwai dubunnan masu digiri a fannin shari’a, fasaha, sha’anin shugabanci, kiwon lafiya, da sauransu a bangaren Kudu.
KU KARANTA: Dattawan Arewa sun gano hanyar shigo da makamai
“90% na ma’aikata Arewa sun fito ne daga yankin Kudu ko mutanen kasar waje.” Don haka ne Arewa ta ga idan aka bada ‘yanci a 1956, ba ta shirya ba.
Yakasai ya yi wannan bayani ne a wata takarda da ya buga game da tarihin kasa domin murnar cika shekara 94 a Duniya a ranar 31 ga watan Disamba.
A gefe guda kun ji cewa dattawa sun kai Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kotu, su na so a hana Jihar Kano cin bashin kudi Naira Biliyan 300 da tayi niyya.
Yanzu an soma shari’a tsakanin wadannan mutane da Abdullahi Ganduje, ana neman takawa gwamna burki wajen cin bashin da ya ke shirin yi daga Sin.
Shi dai Ganduje ya ce aikin jirgin kasa ya ke so ayi da kudin, a 2021 kotu za ta sake sauraron karar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng