Tsaro: Kungiyar dattijan arewa ta tona asirin sabuwar hanyar shigo da makamai yankin

Tsaro: Kungiyar dattijan arewa ta tona asirin sabuwar hanyar shigo da makamai yankin

- Kungiyar dattijan arewa (ACF) ta kwarmata cewa yanzu an koma amfani da Rakuma wajen shigo da makai

- ACF ta bayyana cewa mambobinta daga jihohn Sokoto da Zamfara ne suka sanar da ita hakan

- A cewar ACF, alhakinta ne ta fasa kwai, ta sanar da gwamnatin tarayya domin daukan matakin da ya dacer

Babbar kungiyar zamantakewa da siyasa, kungiyar tuntuba ta arewa (ACF), ta kwarmata cewa yanzu da rakuma ake amfani wajen shigo da makamai yankin arewa.

ACF ta bayyana cewa ana amfani da Rakuma wajen safarar manyan bindigu na RPG da bindigun harbo jirgin sama zuwa Nigeria ta kan iyakokin da ke arewa, kamar yadda Punch ta rawaito.

Cif Audu Ogbeh, shugaban ACF, shine ya bayyana hakan a cikin wani jawabi mai dauke da sa hannunsa wanda ya fitar ranar Alhamis.

KARANTA: An fara gulma da tsegumi bayan fadar shugaban kasa da gwamna Zulum sun yi gum a kan ganawarsu

Cif Ogbeh ya bayyana cewa ana shigo da makaman ne daga makwabciyar kasa, amma bai ambaci sunan kasar ba.

Tsaro: Kungiyar dattijan arewa ta tona asirin sabuwar hanyar shigo da makamai yankin
Tsaro: Kungiyar dattijan arewa ta tona asirin sabuwar hanyar shigo da makamai yankin @Daily Trust
Source: Facebook

Sai dai, ACF ta ce mambobinta daga jihohin Sokoto da Zamfara ne suka sanar da su hakan.

Najeriya ta yi iyaka da kasar Nijar ta bangaren jihohin Sokoto da Zamfara.

KARANTA: Katsina: 'Yan bindiga sun koma cikin fushi bayan guduwar mutane 8 da suka sace, sun sake sace wasu 9

Shugaban na ACF ya bayyana cewa alhakin kungiyar ne ta sanar da gwamnatin tarayya wannan bayani domin daukan matakin da ya dace.

Cif Ogbeh, tsohon ministan noma, ya ce 'yan bindiga na samun kudin siyen makamai daga kudaden biyan fansa da suke tatsa daga hannun jama'a.

Legit.ng ta rawaito cewa tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya yi kira ga 'yan Najeriya tare da kalubalantar Buhari da shugabanni akan su daina dorawa Allah laifin rashin cigaban kasa.

Obasanjo ya bayar da wannan shawara ne a dakin karatunsa mai suna Olusegun Obasanjo Presidential Library dake Abeoluta cikin jihar Ogun a wani sakonsa na shiga sabuwar shekara.

Ya kalubalanci shugaba Buhari da sauran shugabanni su daina dora alhakin halin da Najeriya ke ciki kan Ubangiji, su zargi kansu kurum.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel