Cikakken sunayen shahararrun masu mukaman siyasa 5 da Buhari ya sallama a 2020

Cikakken sunayen shahararrun masu mukaman siyasa 5 da Buhari ya sallama a 2020

Saboda wasu dalilai da ba a bayyana ba, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a wan nan shekarar ta 2020 ya sallami wasu masu rike da mukaman siyasa daga bakin aikinsu.

Kamar yadda ake tsammani, an maye gurbin wadanda aka sallama da wasu.

Yayinda shekarar 2020 ya zo karshe, Legit.ng ta bankado wasu muhimman nade-nade biyar da Shugaban Najeriyan ya soke.

KU KARANTA KUMA: 2023: Jami’an gwamnatin Ebonyi sun bukaci Umahi yayi takarar Shugaban kasa

Cikakken sunayen shahararrun masu mukaman siyasa 5 da Buhari ya sallama a 2020
Cikakken sunayen shahararrun masu mukaman siyasa 5 da Buhari ya sallama a 2020 Hoto: @adsmusterr, @jacksonpbn, @MobilePunch, @IjeomacynthiaA
Asali: Twitter

1. Nasiru Mohammed Ladan Argungu, shugaban hukumar NDE

A ranar Litinin, 7 ga watan Disamba, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami darakta-janar na hukumar daukar ma’aikata (NDE), Nasiru Mohammed Ladan Argungu.

Yayinda ba a bayar da wani dalili na sallamarsa ba, Legit.ng ta lura cewa Argungu ya samu sabani da karamin ministan kwadago da daukar ma’aikata, Festus Keyamo, game da shirin ayyuka 774,000 na musamman.

KU KARANTA KUMA: Nade-naden mukaman siyasa da Shugaba Buhari yayi a yankuna da jihohi (dalla-dalla)

2. Charles Dokubo, jagoran shirin jin kai

A watan Agusta, Shugaba Buhari ya sallami jagoran shirin jin kai a fadar Shugaban kasa, Charles Dokubo.

Shima kakakin Shugaban kasa Garba Shehu bai bayar da wani dalili na sallamarsa ba.

An maye gurbin Dokubo wanda ya kasance Farfesa da Milland Dikio, kanal na rundunar soji mai ritaya.

3. Farfesa Charles Uwakwe, rajistran NECO

Shugaban kasa Buhari ya kuma sallami Farfesa Charles Uwakwe a matsayin rijistran hukumar zana jarrabawar NECO. An sallame shi tare da mataimakan daraktocin hukumar jarrabawar biyu.

Yayinda ba a bayar da wani dalili na sallamar shugabannin ba, rahotanni sun nuna cewa watakila an sallame su ne saboda zargin rashawa.

4. Usman Mohammed, MD na TCN

A watan Mayu, shugaba Buhari ya sallami Usman Mohammed a matsayin manajan daraktan kamfanin TCN.

5. Kemebradikumo Pondei, MD na hukumar NDDC

A watan Disamba, Shugaban kasa Buhari ya sallami Daniel Pondei a matsayin mukaddashin manajan darakta na hukumar ci gaban Niger Delta (NDDC).

Hakan ya kasance ne yayinda Shugaban kasar ya amince da nadin kwamitin wucin gadi da zai kula da harkokin hukumar.

A wani labari, Femi Falana a wata tattaunawa ta intanet ta ASCAB ta shirya ya bayyana cewa talauci yafi Coronavirus saurin kisa a Najeriya.

Yayin da gwamnati ke kokarin kawo rigakafin COVID-19, dole ta samar da hanyoyin kakkabe talauci da sauran cutuka da ke addabar talaka, a cewa Falana.

Ya kara da cewa gwamnati na bawa COVID-19 kulawa ne saboda ba cuta ce da ta shafi talaka ba sai dai masu arziki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng