Nade-naden mukaman siyasa da Shugaba Buhari yayi a yankuna da jihohi (dalla-dalla)

Nade-naden mukaman siyasa da Shugaba Buhari yayi a yankuna da jihohi (dalla-dalla)

Biyo bayan zargin da Bishop Mathew Kukah yayi wa Shugaban kasa Muhaammadu Buhari na son kai, an koma ga tattauna wasu yankuna ne suka fi samun wakilai a nade-naden Shugaban kasar.

Wannan zauren ya kawo bayani dalla-dalla kan nade-nade 190 da Buhari yayi a kwanaki kamar yadda jaridun Premium Times da Daily Trust suka ruwaito.

Jaridun biyu sun yi nuni ga wata takarda daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya.

KU KARANTA KUMA: Kada wani abu ya samu Bishop Kukah, Inji Apostle Suleman

Nade-naden mukaman siyasa da Shugaba Buhari yayi a yankuna da jihohi (dalla-dalla)
Nade-naden mukaman siyasa da Shugaba Buhari yayi a yankuna da jihohi Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Rabe-raben yanki-yanki

1. Kudu maso yamma – Nade-nade 64

2. Arewa maso yamma - Nade-nade 37

3. Arewa maso gabas – Nade-nade 29

4. Kudu maso kudu – Nade-nade 24

5. Arewa maso tsakiya – Nade-nade 21

6. Kudu maso gabas – Nade-nade 15

A matakin jiha, jihar Ogun ce ke da mukaman siyasa mafi yawa da Shugaban kasa Buhari nada tun bayan sake zabensa a 2019 inda take da 17 cikin nade-nade 190 a daidai lokacin wannan rahoton. Kalli rabe-rabensu a kasa.

Rabe-raben Jiha-jiha: Guda biyar da ke kan gaba

1. Jihar Ogun - 17

2. Jihar Adamawa - 14

3. Jihar Kano - 12

4. Jihar Lagos - 12

Dalla-dalla: Kudu da Arewa

1. Yankin kudu (jihohi 17) – Nade-nade 103

2. Yankin Arewa (jihohi 19) – Nade-nade 87

Legit.ng ta tattaro cewa dukkanin nade-naden na aiki a ofishoshin Shugaban kasa, mataimakin Shugaban kasa, uwargidar Shugaban kasa da uwargidar mataimakin Shugaban kasa.

Premium Times ta nusar cewa dakatar ofishin sakataren gwamnatin bai sanya nade-naden da Shugaban kasar yayi a ma’aikatun tarayya (sakatarorin dindindin), hukumomi da masana’antu ba.

Hakazalika ba ya dauke da nade-naden jakadu da na hukumomin tsaron kasar.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Buhari ya gazawa yan Najeriya, Kwande

A wani labari, an matsawa gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi lamba a kan ya fito takarar kujerar Shugaban kasa a 2023.

Mataimakin gwamnan jihar, Kelechi Igwe da sauran mambobin majalisar dokokin jihar sun bukaci Umahi da ya kaddamar da kudirinsa na takarar shugaban kasa.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa jami’an sun ziyarci gwamnan a mahaifarsa da ke Uburu, karamar hukumar Ohaozara don tattauna lamarin tare da shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel