Jonathan ya yi wa Buhari bayanin halin da ake ciki a siyasar Gambia

Jonathan ya yi wa Buhari bayanin halin da ake ciki a siyasar Gambia

- Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari a fadar gwamnati a ranar Talata

- Rahotanni sun bayyanan cewa Jonathan ya ziyarci shugbaan kasar ne don masa bayanin hain da ake ciki a siyasar kasar Gambia

- Goodluck Jonathan ne wakilin kungiyar ECOWAS a kasar Mali kuma ya dade yana aiki don ganin an daidaita siyasar kasar

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, a ranar Talata, ya yi wa shugaba Muhammadu Buhari bayanin irin ci gaban da aka samu game da sha'anin siyasar kasar Gambia, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaba Adama Barrow ya sake neman tsayawa takara duk da kalubale da kuma rashin tabbas.

Barrow an gana da shugaba Buhari ranar 3 ga Disamba a fadar shugaban kasa a Abuja, kuma ya bayyanawa manema labarai cewa kasar sa na bukatar taimakon Najeriya.

Jonathan ya yi wa Buhari bayanin halin da ake ciki a siyasar Gambia
Jonathan ya yi wa Buhari bayanin halin da ake ciki a siyasar Gambia. Hoto: @BashirAhmaad
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Zulum ya karrama bataliyar sojin da Boko Haram bata taba galaba a kanta ba (Hotuna)

"Badan taimakon da kuka bamu ba za a mu sha matukar wahala," inji Barrow.

Jonathan, a wata tattaunawa da ya yi da yan jarida bayan ganawar sirrin, ya ce ya yi wa Buhari bayanin halin da ake ciki game da kudirin sa ga Banjul, babban birnin Gambia.

Jonathan, wanda shi ne wakilin ECOWAS a Mali, ya ce burin sa shi ne ya samar da hanyoyin da za a warware rikicin siyasar Gambia.

Ya ce ya yi nasarar kammala sashen farko na aikin kuma zuwa watan Janairun 2021, za a shawo kan rashin fahimtar siyasa a matsayin sashen karshe na aikin.

DUBA WANNAN: Jam'iyyar PDP a Ondo ta dakatar da jiga-jigan mambobinta biyar

Wasu yan adawa suna zanga zanga, suna masu cewa ya kamata shugaban ya cika alkawarin da ya yi na zango daya da ya ce zaiyi.

Idan za a iya tunawa shugaba Buhari a ranar 3 ga Disamba, ya shaidawa shugaba Barrow lokacin da ya kawo ziyara cewa shi ne ya jagoranci tawagar ECOWAS wajen kakkabe shugaba Yahya Jammeh na Gambia a 2016 don dawo da martabar yankin tare da alkawarin Najeriya zata tallafawa kasar Gambia ta duk hanyoyin da ya kamata yayin da zasu yi zabe shekara mai kamawa

A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.

Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.

Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel