Wata Jami’a ta ba tsohon Shugaban kasa Jonathan lambar yabo a gida
Kwanan nan ne mu ka samu labari cewa an karrama tsohon Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan a wata Jami’a da ke Jihar Ribas. An karrama Jonathan ne saboda kokarin da yayi wa siyasar Najeriya.
Jami’ar ilmi ta Ignatius Ajuru ta Jihar Ribas ta ba tsohon Shugaba Goodluck Jonathan lambar yabo na gwarzon Damukaradiyya a Najeriya a wajen bikin yaye ‘Daliban ta da aka yi a makon nan.
Wannan ne karon farko da Jami’ar ta karrama wani Shugaba a kasar da irin wannan lambar girma da jinjina kamar yadda Shugaban Jami’ar King A.M Ikuru ya bayyana a wajen taron.
Babbar Jami’ar ta zabi Jonathan ne a dalilin irin kokarin da yayi na gudanar da zaben kwarai sannan ya sauka daga kujerar sa ya mikawa Jam’iyyar adawa bayan ya sha kasa a 2015.
KU KARANTA: Rikicin siyasa na nema ta ci PDP a Jihar Kano
Wani babban Farfesa a Jami’ar mai suna Boma Obi yace abin da Jonathan din yayi ba kowane ‘dan siyasa bane zai iya a kasar. Dalilin haka ne aka karrama tsohon Shugaban na Najeriya.
Tsohon Shugaban kasar yai godiya da wannan karramawa da aka yi masa inda yake cewa wata rana zai iya komawa aikin koyarwa a Jami’ar kamar yadda ya fara a malanta rayuwar sa.
Wannan Jami’a ta karrama tsohon Shugaban ne da kuma Mai dakin sa Patience Jonathan. Yanzu haka an sanyawa wani dakin karatu sunan Uwargidan tsohon Shugaba Jonathan.
Shi kuma daya daga cikin manyan ‘Yan takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar adawa ta PDP Ibrahim Dankwambo ya bayyana cewa yana da duk abin da ake bukata wajen mulkin kasar nan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng