2023: Jami’an gwamnatin Ebonyi sun bukaci Umahi yayi takarar Shugaban kasa

2023: Jami’an gwamnatin Ebonyi sun bukaci Umahi yayi takarar Shugaban kasa

- Yan siyasan Najeriya sun fara shirye-shirye don zaben shugaban kasa na 2023

- Wasu jami’an gwamnatin jihar Ebonyi sun bayyana dalilin da yasa Gwamna Dave Umahi ya dace da takarar shugaban kasa

- Gwamnan ya fada ma mutanen kudu maso gabas abunda za su samu idan suka marawa APC baya

An matsawa gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi lamba a kan ya fito takarar kujerar Shugaban kasa a 2023.

Mataimakin gwamnan jihar, Kelechi Igwe da sauran mambobin majalisar dokokin jihar sun bukaci Umahi da ya kaddamar da kudirinsa na takarar shugaban kasa.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa jami’an sun ziyarci gwamnan a mahaifarsa da ke Uburu, karamar hukumar Ohaozara don tattauna lamarin tare da shi.

2023: Jami’an gwamnatin Ebonyi sun bukaci Umahi yayi takarar Shugaban kasa
2023: Jami’an gwamnatin Ebonyi sun bukaci Umahi yayi takarar Shugaban kasa Hoto: @EbonyiGov
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Sojoji 3 sun mutu, da dama sun jikkata sakamakon tashin abubuwan fashewa da Boko Haram suka binne

Da yake magana a madadin sauran jami’an, mataimakin gwamnan ya ce sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) saboda Umahi.

Ya ce:

“A sanda ka sanar cewar lokaci yayi da za a tafi gaba, da yawa daga cikinmu muna ta jan kafa, muna ta son tattaunawa amma a karshe, sai muka yanke shawarar tafiya da kai. Dole in fada maka gaskiya cewa wasunmu basu so APC ba amma muka yanke shawarar komawa saboda kai. Don haka, muna kaddamar da cewa dole ka tsaya takarar kujerar Shugaban kasa.”

Gwamnan, a martaninsa ya bukaci jami’an da su ci gaba da ba APC goyon baya. Ya ce jam’iyyar ta samar da wata kafa ga yan Igbo domin su kimanta kansu da kyau.

Sai dai Umahi bai bayyana ko zai yi takarar Shugaban kasa a zaben 2023 ba.

KU KARANTA KUMA: Seth Sincere, dan kwallo na Najeriya, ya kammala ginin gidansa na miliyoyin naira a Abuja

A wani labarin, majalisar Kansiloli ta tsige Shugaban Ƙaramar Hukumar Shiroro, Kwamred Dauda Suleiman Chukuba, bisa zargin Almundahana.

A cewar majalisar, sun bawa shugaban duk wata dama domin ya kawar kansa daga zargin da ake yi masa amma sai ya nuna musu raini.

Ana zargin Kwamred Chukuba da yin almubazzaranci da barnatar da kudaden shiga da karamar hukuma ta samu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng