2023: Mutane 5 da ka iya maye gurbin Buhari daga kudu maso gabas

2023: Mutane 5 da ka iya maye gurbin Buhari daga kudu maso gabas

- Ana ci gaba da tattauna yadda tseren kujerar shugaban kasa zai kasance

- Koda dai masana harkokin siyasa da dama sun yi korafin cewa yayi wuri da za a fara mayar da hankali kan daga inda Shugaban kasa na gaba zai fito

- Legit.ng ta lissafo wasu shugabannin Igbo da ka iya gadar shugaba Buhari a zaben 2023

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), mai mulki na iya mika tikitin takarar Shugaban kasarta zuwa yankin kudu bayan karewar wa’adin mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari,

Koda dai ana ta rade-radin cewa manyan yan kasar ciki harda jigon APC na kasa Bola Tinubu da Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti na hararar kujerar.

Akwai zazzafan muhawarar cewa tunda Yarbawa sun samar da Shugaban Najeriya, ya kamata yan Igbo su karbi shugabanci saboda adalci.

2023: Mutane 5 da ka iya maye gurbin Buhari daga kudu maso gabas
2023: Mutane 5 da ka iya maye gurbin Buhari daga kudu maso gabas Hoto: @OUKtweets/@realRochas
Asali: Twitter

Yayinda ake ci gaba da tattauna tseren na 2023, Legit.ng ta jero wasu mutane biyar da ake ganin za su gaji Buhari idan APC da PDP suka yanke shawarar mikawa kudu maso gabas tikitin takara.

KU KARANTA KUMA: Sojoji 3 sun mutu, da dama sun jikkata sakamakon tashin abubuwan fashewa da Boko Haram suka binne

1. Orji Uzor Kalu

Tsohon gwamnan jihar Abia kuma bulaliyar majalisa mai ci a yanzu, Sanata Kalu ya kasance daya daga cikin yan takarar da ke kan gaba da ake ganin sun dace da hawa kujerar daga kudu maso gabas.

Harma matasa daga kudu maso gabas da sauran yankunan kasar sun fara nuna goyon bayansu ga jigon na APC wanda ya kuma kasance Shugaban Igbo a tseren.

2. Chris Ngige

Ministan kwadago da diban ma’aikata, Ngige ya kasance daya daga cikin shugabannin kudu maso gabas a jam’iyya mai mulki.

Ya kuma yi aiki a matsayin tsohon gwamnan Anambra sannan aka zabe shi a matsayin sanata mai wakiltan Anambra ta tsakiya a 2011.

Babban jigo a majalisar Shugaban kasar, ana ganin Ngige na iya darewa kujerar mafi daraja a kasar.

3. Gwamna Dave Umahi

Mutane da dama sun yi hasashen cewa gwamnan jihar Ebonyi mai ci wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki a kwanan nan ya koma jam’iyyar ne saboda shirin 2023.

An kuma bayyana Umahi wanda ya kasance shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas, a matsayin daya daga cikin mutanen da za su gaji shugaba Buhari a 2023.

4. Rochas Okorocha

Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha,ya kasance daya daga cikin wadanda za su ci moriyar abun idan har aka mika wa yankin kudu maso gabas tikitin takarar Shugaban kasar a 2023.

Wata kungiya a ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamba, ta bukaci tsohon gwamnan da ya nemi tikitin takarar Shugaban kasar.

Okorocha ya kasance makusancin Shugaban kasar kuma ana sanya ran zai shiga tseren.

5. Peter Obi

Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya kasance daya daga cikin manyan yan takarar da ake ganin zai zama Shugaban kasa daga kudu maso gabas.

Fitaccen dan kasuwa kuma masanin tattalin arziki, Obi ya kasance dan takarar mataimakin Shugaban kasa a zaben da aka yi na karshe, inda yayi takara tare da Atiku Abubakar.

KU KARANTA KUMA: Seth Sincere, dan kwallo na Najeriya, ya kammala ginin gidansa na miliyoyin naira a Abuja

A gefe guda, mun ji cewa an matsawa gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi lamba a kan ya fito takarar kujerar Shugaban kasa a 2023.

Mataimakin gwamnan jihar, Kelechi Igwe da sauran mambobin majalisar dokokin jihar sun bukaci Umahi da ya kaddamar da kudirinsa na takarar shugaban kasa.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa jami’an sun ziyarci gwamnan a mahaifarsa da ke Uburu, karamar hukumar Ohaozara don tattauna lamarin tare da shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel