Seth Sincere, dan kwallo na Najeriya, ya kammala ginin gidansa na miliyoyin naira a Abuja

Seth Sincere, dan kwallo na Najeriya, ya kammala ginin gidansa na miliyoyin naira a Abuja

- Seth Sincere ya kasance dan kwallon kafa na Najeriya wanda a yanzu yake bugawa Boluspor wasa a kasar Turkiyya

- Dan wasan mai shekaru 22 ya gina wa kansa da iyalansa wani katafaren gida a Abuja

- Sincere ya buga wa Najeriya wasanni shida na yan kasa da shekaru 23

Tsohon dan kwallon Najeriya na yan kasa da shekaru 23 Seth Sincere ya kammala ginin wani katafaren gida na miliyoyin naira a babbar birnin tarayya Abuja.

A watan Satumban shekarar da ta gabata, Seth Sincere ya sake samun wata gayyata domin bugawa Najeriya wasa na yan kasa da shekaru 23 a gasar Olympic inda suka kara da Sudan wanda aka yi a Asaba, jihar Delta.

Kasancewar ya buga wa kungiyar wasanni biyar a baya, Seth Sincere ya yi farin ciki da damar da ya sake samu na bugawa tawagar wasa duk da cewar Najeriya bata samu shiga gasar ta Olympic ba.

Seth Sincere, dan kwallo na Najeriya, ya kammala ginin gidansa na miliyoyin naira a Abuja
Seth Sincere, dan kwallo na Najeriya, ya kammala ginin gidansa na miliyoyin naira a Abuja Hoto: @simplykemkem
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Kukah: Ban yi kira ga juyin mulki a kan gwamnatin Buhari ba, limamin Katolika ya fayyace gaskiya

A bisa ga wallafar da mai kawo rahoton wasanni Nelson yayi a shafin soshiyal midiya, Seth Sincere ya gina katafaren gida a Garki da ke Abuja.

Ya wakilci Najeriya a gasar Afrika na 2015, gasar cin kofin Afrika na yan kasa da shekaru 23 da gasar Olympics na 2015.

Ana ta kira kan a gayyaci Seth Sincere cikin kungiyar Super Eagles duba ga tarin kokarinsa a wannan kakar wasa na Boluspor a Turkiyya.

Zuwa yanzu, Seth Sincere ya buga ma Boluspor wasanni 19 sannan bai jefa kowani kwallo ba a ragata bangaren Turkiyyan.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa 2023: Primate Ayodele ya ce Allah bai aiko Tinubu don ya shugabanci Najeriya ba

A wani labarin, an fito da jerin ‘yan wasan kwallon kafan da ba a taba yin irinsu ba. France Football ce tayi wannan aiki da taimakon wasu kwararrun ‘yan jarida 140.

Jaridar The Sun ta ce an zabi rukunin ‘yan wasa 11 har kashi uku. Irinsu Cristiano Ronaldo da Lionel Messi suna cikin sahun farko na jerin taurarin.

Rahoton ya tabbatar da cewa tsofaffin ‘yan wasa Pele da marigayi Diego Maradona sun samu shiga wannan sahu, amma babu wurin Zinedine Zidane.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng