Sojoji 3 sun mutu, da dama sun jikkata sakamakon tashin abubuwan fashewa da Boko Haram suka binne

Sojoji 3 sun mutu, da dama sun jikkata sakamakon tashin abubuwan fashewa da Boko Haram suka binne

- An rahoto cewa mayakan Boko Haram sun kashe sojoji uku a jihar Borno

- Jami’an tsaron na Najeriya sun mutu ne bayan sun shiga abubuwan fashewa da yan ta’addan suka binne a karkashin kasa

- An tattaro cewa sojoi da dama sun ji munanan raunuka a lamarin da ya lalata motocin sojin gaba daya

Akalla jami’an rundunar sojin Najeriya uku ne suka mutu sakamakon tashin abubuwan fashewa da yan ta’addan kungiyar Boko Haram suka dasa a karkashin kasa.

A bisa ga rahoton kafar labarai abun dogaro, an kashe sojojin ne a hanyar Maiduguri/Gomboru a ranar Litinin, 28 ga watan Disamba, lokacin da ayarin motocin rundunar bataliya ta uku suka yi tawo mu gama da abubuwan fashewar.

An tattaro cewa sojojin na raka matafiya tsakanin Gomboru Ngala da Dikwa lokacin da suka yi tawo mugama da abubuwan fashewar wanda yayi sanadiyar mutuwar mutum uku da jikkata wasu da dama.

Sojoji 3 sun mutu, da dama sun jikkata sakamakon tashin abubuwan fashewa da Boko Haram suka binne
Sojoji 3 sun mutu, da dama sun jikkata sakamakon tashin abubuwan fashewa da Boko Haram suka binne Hoto: @DefenseNigeria
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Seth Sincere, dan kwallo na Najeriya, ya kammala ginin gidansa na miliyoyin naira a Abuja

Wani soja da abun ya faru a idonsa ya ce motocin, wanda ke dauke da sojoji, ya lalace ta yadda ba za a iya gyarawa ba.

“Motarsu na yaki ya lalace fiye da tsammani sannan mun rasa wasu sojoji sakamakon tashin abubuwan fashewa da aka binne a karkashin kasa a hanyar Dikwa/Gomboru da Ngala.

“Addu’anmu da tunaninmu na tare da iyalansu. Abun bakin ciki ne, mun rasa sojoji uku saboda abun fashewa.”

Rundunar sojin Najeriya bata fitar da kowani sanarwa kan mutuwar sojojin ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa 2023: Primate Ayodele ya ce Allah bai aiko Tinubu don ya shugabanci Najeriya ba

A gefe guda, mun ji cewa an ceto mutane 23 da suka hada da kananan yara da mata wanda yan bindiga suka yi garkuwa da su a wata musayar wuta a Jihar Katsina.

Yan bindiga shida aka kashe yayin musayar wutar tare da gano dabbobin da suka sace da kuma babura harma da bindiga.

Kakakin yam sandan jihar ya bayyana cewa sun yi wa yan bindigar kawanya bayan sun sami labarin gaggawa na harin da suka kai kauyen Lambo a Kurfi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: