COVID-19, Beirut, Zaben Amurka, Iran da sauran abubuwan da suka faru a bana

COVID-19, Beirut, Zaben Amurka, Iran da sauran abubuwan da suka faru a bana

-Ana ganin ba a taba yin shekarar kamar 2020 a cikin karnin bayan nan ba

-A wannan shekara ne aka samu labarin COVID-19 da ta kashe Bayin Allah

-Haka zalika an yi zaben shugaban kasa da ya ba Jama’a mamaki a Amurka

Masana tarihi su na cewa shekarar 2020 ta zo da abubuwa da dama wanda aka dade ba a gani ba a Duniya, daga ciki har da annobar COVID-19.

Punch ta tattaro abubuwa da su ka faru a wannan shekara wanda su ka sa ta sha ban-bam da sauran shekarun da suka wuce a wannan marra.

Ga jerin wasu daga cikin abubuwan da jeridar ta ambata:

1. COVID-19

A wannan shekara ne annobar Coronavirus ta ratsa Duniya bayan ta bullo daga kasar Sin. Kusan mutum miliyan 1.8 wannan cuta ta hallaka yanzu.

2. Zaben Amurka

A shekarar bana ne aka gudanar da zaben shugaban kasa a Amurka, inda shugaba Donald Trump ya sha mamaki a hannun ‘dan adawa, Joe Biden.

3. GSSS Kankara

Haka zalika a wannan shekara ne ‘yan bindiga su ka shiga wata makarantar sakandare a garin Kankara, Katsina, su ka yi awon gaba da yara 340.

4. Rigimar Iran

Shekarar nan ta fara ne da kisan babban jagoran sojojin Iran, Janar Qasem Soleimani. Amurka ce ta ke da laifin wannan kisan da ya nemi ya jawo rigima.

KU KARANTA: ASUU ta janye yajin-aikin watanni 9 a Najeriya

5. BREXIT

A watan Junairu kasar Birtaniya ta kafa tarihin zama ta farko a nahiyar Turai da ta tsere daga kungiyar EU. Tun shekarar 2016 aka fara wannan yunkuri.

6. Amurka da Taliban

Kasar Amurka ta shiga yarjejeniya da ‘Yan Taliban a karshen Fubrairun bana. Wannan ya sa aka cin ma matsayar kasashen waje za su bar Afghanistan a 2021.

7. Kisan George Floyd

Wani bakin mutumi da jami’an tsaro su ka hallaka a kasar Amurka ya jawo zanga-zanga daga ko ina a fadin Duniya, ana tir da masu nuna wariyar launin fata.

8. EndSARS

Fafutuka da gwagwarmyar #EndSARS da aka fara a Najeriya ta shiga ko ina ta dandalin sada zumunta. Taurarin Duniya duk sun fito sun ba tafiyar armashi.

KU KARANTA: Buhari: Gwamnati za ta shawo kan tsadar abinci a shekara mai zuwa

COVID-19, Beirut, Zaben Amurka, Iran da sauran abubuwan da suka faru a bana
Shugaban Najeriya da takunkumi Hoto: www.africanews.com
Asali: UGC

9. Bam a Beirut

A ranar 4 ga watan Agustan 2020 ne wani bam ya tarwatse a garin Beirut. Wannan bam ya yi sanadiyyar kashe mutane fiye da 200, ya raunta akalla 6, 500.

10. Amurka v Sin

2020 ba ta kare haka nan ba sai da aka yi ‘yar rigima tsakanin Amurka da kasar Sin, inda kasar ta Amurka ta ke zargin Sinawa da laifin barkewar COVID-19.

Duk a wannan shekara ne kuma aka yanka wasu Manoma a jihar Borno. Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin wannan harin da aka kai a garin Zabarmari.

Manoman shinkafa 78 da ake zargin an yi wa yankan-rago a garin na Zabarmari da ke jihar Borno.

Ana ganin cewa wannan ta'adi da 'yan ta'addan su ka yi a yankin Jere, ya na cikin mafi munin barnar da Mayakan Boko Haram su ka yi cikin tsawon shekaru.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel