Zaben 2023: PDP za ta kwace mulkin Najeriya daga hannun Buhari – Bala Mohammed

Zaben 2023: PDP za ta kwace mulkin Najeriya daga hannun Buhari – Bala Mohammed

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya bayyana cewa jam'iyyarsu ta Peoples Democratic Party (PDP), za ta lashe zabe a 2023.

A wata hira da gwamnan ya yi da sashin Hausa na BBC, ya ce kawunan yan jam'iyyar APC duk a rarrabe yake, cewa sun hadu ne ta wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari kawai.

Da aka tambaye shi kan yadda yake ganin zaben PDP a 2023, Gwamna Bala ya ce: “Mu dai mun san jam’iyyar APC hadin gambiza ce, na mutane wanda suke mayaudara, kuma wanda su zo suka hada kawunansu daga wurare daban-daban, kuma wanda suke har yanzu kansu a rarrabe ne.

"Abunda ya hada su kawai mutum daya ne, shine mai gida Muhammadu Buhari shugaban kasa. Kuma zai gama mulkinsa a 2023, saboda haka abunda ya hadasu ya raba. Yanzu ka ga kowa yana magana a kan zama shugaban kasa duk kansu a rarrabe.

Zaben 2023: PDP za ta kwace mulkin Najeriya daga hannun Buhari – Bala Mohammed
Zaben 2023: PDP za ta kwace mulkin Najeriya daga hannun Buhari – Bala Mohammed Hoto: Premium Times
Asali: UGC

"Mu kuma yanzu a PDP dama jam’iyya ce wacce take kanta a hade, ta goge a harkar mulki kuma mun yi kuskure iri-iri, kuma wasu kuskurenmu bai kai ba amma saboda farfaganda na karya yau ga abunda yake faruwa a NDDC da EFCC wanda aka yi mana karya, amma mun gode mutanen Najeriya basu yarda da wannan kazafin da aka mana ba suka zabe mu.

"Yau ga abunda yake faruwa a cikin gwamnatin, a cikin fadar gwamnati yadda ya kasance manyan mutane ana ganinsu da takun rashawa har sun nutse iya wuya.

"Saboda haka, kuma yau ga maganar tsaro, da ance mune Boko Haram toh yanzu wanene Boko Haram din? Har gwamna ma ake so a kashe, mu kuwa bamu taba samun wannan ba a lokacinmu na PDP. Abune na karya na yaudara kuma ance karya fure take bata ‘ya’ya.

"Yan Najeriya sun gani a kasa kuma sun san cewa jiki magayi, ana jin yunwa, ana ganin wahala, kasuwanci duk ya karye, kuma maganar fada da rashawar ma ace sune masu rashawa din fiye da kowa.

"Da izinin Allah mutanen Najeriya idanunsu ya bude kuma rana ya fito, duhu ya yaye kuma duk ina ganin 2023 da zai zo mutanen Najeriya za su zabi PDP.

Da aka tambaye shi ko yana ganin PDP bata da nata matsaloli na cikin gida irin na APC, ya ce : “Mu bamu da matsaloli, inda muka samu tazara a kan APC shine mu jiki magayi ne, muna mun yi kuskure a baya na dauko mutane wadanda basu cancanta ba a sa ko kuma kama karya, toh mu mun ganta.

"Amma yanzu su suke yinta, ka ga kamar yadda aka hada gwamnan Lagas mai karfi, ka ga yadda ya faru a jihar Zamfara, yadda aka sa aka yi son zuciya PDP ta dawo, ko a nan jihar Bauchi haka anyi son zuiya shine Allah ya sa muka dawo.

"Yanzu haka jam’iyyar bata da shugabanni sai dai an kawo na wucin-gadi wanda shima gwamna ne, to ka ga duk jam’iyyar da ta fara rawar kafa ina tsammanin ba za ta kai ba saboda gurguwa ce."

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 12 da ya kamata ku sani game da marigayi Sanata Buruji Kashamu

Gwamnan ya kuma jadadda cewa akwai kyakyawar alaka tsakaninsu da gwamnonin APC a gwamnatance, sani da kuma fahimtar menene gwamnati. Ya ce su masu da’a ne ga gwamnatin tarayya don sun san girmanta.

Ya kuma yi godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya ce za su ci gaba da basa hadin kai a matsayinsu na gwamnonin PDP.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel