Zargin tsokana: Dino Melaye ya fada ma Buhari cewa kada ya kama Bishop Kukah

Zargin tsokana: Dino Melaye ya fada ma Buhari cewa kada ya kama Bishop Kukah

- Sunan Limamin cocin Katolika na Sokoto, Mathew Kukah ya hau kanen labarai a yan kwanakin nan bayan ya zargi Shugaba Buhari da son kai

- Dino Melaye, tsohon sanata, ya yi martani a kan kiran da wata kungiya tayi na neman a kama malamin

- Dan siyasan ya bayyana dalilin da ya sa ba zai kyautu ayi amfani da yan sanda a kan malamin ba

Dino Melaye, tsohon sanata, ya gargadi Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan yunkurin kama limamin Katolika na Sokoto, Mathew Kukah, kan sukar gwamnati mai ci.

Wasu kungiyoyi a kasar sun caccaki limamin kan zargin Shugaba Buhari da son kai.

Kungiyar matasan Tiv sun zargi limamin da kira ga tunkudar da shugaban kasar sannan suka bukaci hukumomin tsaro su binciki malamin.

Zargin tsokana: Dino Melaye ya fada ma Buhari cewa kada ya kama Bishop Kukah
Zargin tsokana: Dino Melaye ya fada ma Buhari cewa kada ya kama Bishop Kukah Hoto: Premium Times, Muhammadu Buhari - Facebook
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun yi garkuwa da Limamin Katolika da direbansa a Imo

Sai dai, Melaye ya bayyana cewa daukar irin wannan matakin a kan shugaban addinin zai haddasa tsangwama daga mutane.

Ya yi gargadin cewa idan aka kama Kukah, za a nuna wa Shugaban kasar cewa mutane ne ke da gwamnati ba shi ba.

Ya wallafa a shafinsa:

"Kama ko kayi kokarin tozarta Bishop Kukah mu kuma za mu nuna maka cewa ba kaine ke da gwamnati ba face mutane. Suna son tsoratar da kowa. Ba zai yiwu ba. Kashe tsoro sannan ka fada wa masu mulki gaskiya."

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kai hari garuruwa 6 a Katsina, sun yi garkuwa da mutum 50 harda sabbin ma’aurata

A wani labarin kuma, mun ji cewa kungiyar CAN ta Kiristocin Najeriya ta fito ta kare babban limaminta a Sokoto, Bishof Mathew Hassan Kukah.

Kungiyar ta CAN ta ce a jawabin da Mathew Hassan Kukah ya yi na bikin Kirismeti, babu inda ya soki Musulunci ko kuma ya yi kiran ayi juyin-mulki.

CAN ta zargi gwamnatin tarayya, shugaban kasa da kuma shugaban kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola da neman juya maganar da Faston ya yi.

Wannan jawabi da CAN ta yi, ya fito ne daga bakin mataimakin shugabanta na duka jihohin Arewacin Najeriya, Rabaren John Hayab jiya a Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel