Yan bindiga sun yi garkuwa da Limamin Katolika da direbansa a Imo

Yan bindiga sun yi garkuwa da Limamin Katolika da direbansa a Imo

- Wani shahararren dan Najeriya ya sake shiga hannun masu garkuwa da mutane

- A wannan karon, abun ya cika ne da wani limamin Katolika a Owerri, jihar Imo

- An tsinci kayan bishop din a kusa da Assumpta Cathedral da ke Owerri

Yan sa’o’i bayan Mathew Kukah ya yi korafi a kan halin da kasar ke ciki, yan Najeriya sun sake samun labari mai cike da damuwa da ke nuna cewa babu wanda ya tsira a kasar.

A wannan karon, limamin Katolika na Owerri da ke jihar Imo, Moses Chikwe ne ya shiga hannun yan bindigan.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar APC ta yi zargin cewa majalisa na shirin tsige Buhari da daura Osinbajo

Yan bindiga sun yi garkuwa da Limamin Katolika da direbansa a Imo
Yan bindiga sun yi garkuwa da Limamin Katolika da direbansa a Imo Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A cewar jaridar Premium Times, an yi garkuwa da malamin ne a yankin World Bank da ke Owerri, babbar birnin jihar. An tattaro cewa an sace shi ne tare da direbansa.

A cewar kafar labaran, an tsinci mota da tufafin malamin a kusa da Assumpta Cathedral da ke Owerri.

Sakatariyar Katolika ta Najeriya ta ce Archbishop na Diocese, Victor Obinna, ya tabbatar da sace malamin.

Cocin ya kuma yi kira ga addu’a don dawowarsa lafiya.

KU KARANTA KUMA: Dattawan arewa sun yi martani ga kiran Kukah na yiwa gwamnatin Buhari juyin mulki

A wani labarin, wasu yan bindiga da ake zaton masu fashi da makami ne sun jefa wasu garuruwan Katsina cikin bakin ciki bayan sun yi garkuwa da kimanin mutane 50.

Yan fashin wadanda suka kai hari kan al’umman sun kuma kashe mutum biyu a yayin mamayar da suka kai yankin Batsari da ke jihar Katsina a karshen mako.

Wasu daga cikin garuruwan da suka kai hari sun hada da Daurawa, Kasai, Biya-ka-Kwana, Bakon Zabo, Tudun Modi, Watangadiya da sauransu, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng