Kungiyar APC ta yi zargin cewa majalisa na shirin tsige Buhari ta daura Osinbajo

Kungiyar APC ta yi zargin cewa majalisa na shirin tsige Buhari ta daura Osinbajo

- Wata kungiya ta ce ta gano wani makirci da mambobin majalisar dokokin tarayya ke kullawa don tsige Shugaba Muhammadu Buhari

- Sai dai, ta ce za ta yi amfani da duk wata dama na siyasa da take da shi don hana abun da ka iya jefa kasar cikin rikici

- Kungiyar ta kuma yi kira ga murabus din shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawal cikin gaggawa

Wata kungiya ta yi zargin cewa mambobin majalisar dokokin tarayya na shirin tsige Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Da take magana ta wani jawabi a ranar Litinin, 28 ga watan Disamba, kungiyar, Core All Progressives Congress Supporters Network (Co-APC-SuN), ta bayyana kulla kullan a matsayin “ba abun yarda ba, abun bankyama, tozarci kuma abun Allah wadai.”

Ta kuma yi kira ga tsige Shugaban Majalisar dattawa, Ahmad Lawan, wanda ya kuma kasance shugaban NASS na tara, jaridar The Sun ta ruwaito.

Kungiyar APC ta yi zargin cewa majalisa na shirin tsige Buhari da daura Osinbajo
Kungiyar APC ta yi zargin cewa majalisa na shirin tsige Buhari da daura Osinbajo Hoto: @BashirAhmad
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kai hari garuruwa 6 a Katsina, sun yi garkuwa da mutum 50 harda sabbin ma’aurata

Kungiyar, wacce tayi magana ta kakakinta Alhaji Bala Abubakar, ta kuma sha alwashin cewa za ta yi amfani da duk wata dama da take da ita wajen sanya idanu sosai kan tattaunawar siyasa na shugaban majalisar dattawan.

Ta kuma yi kira ga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), mambobin APC a NASS da sauransu a kan su zamo masu lura “domin dakile yunkurin sannan kada su bari a jefa Najeriya a rikicin siyasa.

“Mun ji daga tushe abun dogaro cewa wadannan mutane a jam’iyyar sun kammala shiri tare da hadin gwiwar masu adawa a majalisa domin maye gurbin Shugaba Buhari da mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, wanda ake sanya ran zai kammala shekaru biyu da suka yi wa Buhari saura a matsayin shugaban kasa sannan ya mika mulki.

“Ya kasance yunkuri na take damokradiyyar Najeriya, haddasa rashin tsari a siyasa. Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen amfani da duk wani karfi na doka da muke dashi don hana wasu jagorantar kasar ta kofar baya ba, maimakon sanannen tsari na kada kuri’a."

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Arewa ta nemi a kama Kukah sannan a hukunta shi kan furucinsa game da Buhari

A wani labarin, mun ji cewa Kukah, ya sha caccaka kan sukar gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi a sakonsa na Kirsimeti.

Kungiyar dattawa arewa ta NEF ta ga laifin malamin kan cewa da yayi a tsige Shugaban kasar ta tsarin da baya bisa damokradiyya.

Kukah a martaninsa kan hare-hare da kasha kashe da ake yi a kasar, ya ce idan da Musulmin da ba dan arewa bane Shugaban kasa sannan ya aikata abunda Buhari ya aikata, toh da an yi juyin mulki da dadewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel