Gwamna Zulum ya ziyarci garuruwan da Boko Haram suka kai hari, ya dauki tsatsauran mataki

Gwamna Zulum ya ziyarci garuruwan da Boko Haram suka kai hari, ya dauki tsatsauran mataki

- Yayinda ake ci gaba da yaki da ta’addanci, Boko Haram ta kai hari karamar hukumar Hawul a jihar Borno

- An kashe mutane uku, yayinda aka lalata ofishin yan sanda, shagunan kasuwa da sauran wurare a yayin harin

- Gwamnan jihar, Babagana Zulum, wanda ya kasance a wajen gari, ya takaita tafiyarsa sannan ya ziyarci garuruwan da abun ya shafa cikin gaggawa

- Zulum ya yi umurnin cewa a sake gina kadarorin da aka lalata sannan a samar da motocin fatrol

Gwamna Babagana Umara Zulum ya ziyarci garuruwan da Boko Haram suka kai hari a karamar hukumar Hawul da ke kudancin Borno, a ranar Lahadi, 27 ga watan Disamba.

Gwamnan ya je Abuja don aiwatar da wasu jerin ayyuka amma sai ya takaita tafiyar sannan ya koma jiharsa a safiyar ranar Lahadi.

Harin na ranar Asabar ya shafi akalla garuruwa hudu da suka hada da Tashan Alade, Shafa, Azare, Sabon-Kasuwa da Debro. Hatta ga makarantu, shaguna da wuraren bauta basu tsira ba a harin.

Gwamna Zulum ya ziyarci garuruwan da Boko Haram suka kai hari, ya dauki tsatsauran mataki
Gwamna Zulum ya ziyarci garuruwan da Boko Haram suka kai hari, ya dauki tsatsauran mataki Hoto: The governor of Borno state
Source: Facebook

Yan ta’addan sun sace dubban buhuhunan kayan gona da manoma suka nome kwanan nan sannan suka debe kayayyaki a shaguna da kantunan kasuwa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe jigon PDP, sun yi garkuwa da yayansa mata su 3

An kashe mutum uku a Shafa, biyu daga cikinsu sun kasance maharba da kuma dan farar hula daya.

Gwamna Zulum wanda ya zagaya don duba barnar da yan ta’addan suka yi ya yi umurnin cewa a sake ginasu a nan take.

Domin karfafa tsarin tsaro a garin Shafa, gwamnan ya bayar da umurnin samar da motocin fatrol shida da sauran kayayyakin amfani.

Ya kuma yi umurnin samar da motocin lura ga maharba da yan banga a Yamirshika.

Gwamnan ya kuma ce ya ziyarci garuruwan ne domin karfafa su da kuma samar da tallafi ga yan sa kai da ke ba hukumomin tsaro gudunmawa wajen dawo da zaman lafiya.

A cewarsa, gwamnatinsa za ta ci gaba da mayar da hankali wajen kare rayuka da dawo da zaman lafiya a jihar Borno.

A wani labarin, mazauna kauyukan karamar hukumar Hawul da Boko Haram suka ragargaza sun fara komawa gida.

KU KARANTA KUMA: Jihar Kebbi: Abubuwa 9 da Hisbah ta wajabta da haramta aikata su a Yauri

Mayakan ta'addancin sun kai hari kauyukan inda suka kone majami'u biyu a ranar Kirsimeti.

Sun bayyana yadda suka kwana a cikin dajika da tsaunika a yayin gudun ceton ransu yayin harin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel