Hadiza Gabon ta gwangwaje tsohon da yace yana sonta

Hadiza Gabon ta gwangwaje tsohon da yace yana sonta

- Hadiza Aliyu Gabon ta yi wa wani dattijo da ya nuna yana kaunarta gagarumin kyauta

- Fitaciyyar jarumar ta Kannywood a bai wa dattijon kyautar kudi har naira dubu dari biyu

- Dattijon ya nuna tsananin farin ciki tare da janyewa

Shahararriyar jarumar nan ta Kannywood, Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da Gabon ta yi wa wani dattijo da ya nuna yana kaunarta sha tara ta arziki.

Jarumar ta yi wa dattijon wanda ba a bayyana sunansa ba kyautar kudi har naira dubu dari biyu.

Hakan ya faranta ran tsohon har ya bayyana cewa ya janye tare da yi mata fatan alkhari da tarin addu’o’i.

Hadiza Gabon ta gwangwaje tsohon da yace yana sonta
Hadiza Gabon ta gwangwaje tsohon da yace yana sonta Hoto: Northflix blog
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: Kirsimeti: Ndume ya yi Allah wadai da hare-haren Boko Haram suka kai kauyukan Borno da Adamawa

A wata wallafa da shafin Jakadiyyan_arewa_tv_ ta yi a Instagram, an jiyo dattijon na cewa:

“Alhamdulillah ma shaa Allah, Hajiya Hadiza na ga sako nagode Allah ya saka da alkhairi, ubangii Allah ya bar zumunci kuma kamar yadda kika mun Allah ya miki da alkhairi.

“Kuma kamar yadda kika fada idan biki ya zo za a sanar dani, hakika na yarda na zama uba nagari, albarkar annabi ina daya daga cikin uba iin shaa Allah ranar biki, Allah ya nuna mana lokaci.

“Na karbi kudi naira dubu gari biyu Allah ya saka da alkhairi, Allah ya ji kan mahaifa, nagode, Allah ya kara kusanci da hazaka.

“Da farko dai dattijon ya nuna ra’ayinsa na son jarumar, inda ya roki Allah ya mallaka masa ita a matsayin matarsa ta sunnah.”

KU KARANTA KUMA: Gbajabiamila ya mika ta’aziyya ga iyalan Sheikh Lemu da na Kwankwaso

A wani labari, Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Maryam Booth, ta tabbata a gwarzuwar jarumar Africa Movie Academy Awards, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Maryan Booth ta samu nasarar ne sakamakon rawan da ta taka a wani fim mai suna The Milkmaid, inda ta bige Chairmaine Mujeri (Mirage), Linda Ejiofor (4th Republic) da wasu mutane hudu.

A cike da murnar wannan nasarar, jarumar ta wallafa rubutu a shafinta na Instagram kamar haka: "Ina taya kaina da iyalan fim din milkmaid murna. Muna fatan karin nasarori, sai mun hadu nan gaba a Oscar."

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel