Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe jigon PDP, sun yi garkuwa da yayansa mata su 3

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe jigon PDP, sun yi garkuwa da yayansa mata su 3

- Wasu da ake zaton yan bindiga ne sun jefa al’umman Bosso da jihar Niger cikin rudani da fargaba

- Hakan ya kasance ne sakamakon kisan jigon PDP, da yan bindiga suka yi a ranar Alhamis, 24 ga watan Disamba

- An kuma yi garkuwa da yaran Mohammed wanda ya kasance shahararren dan kasuwa kuma manomi su uku

Tsoro ya kama mutanen karamar hukumar Bosso da ke jihar Niger sakamakon kisan Alhaji Ahmodu Mohammed, jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

An tattaro cewa yan bindiga ne suka kashe Mohammed a ranar Alhamis, 24 ga watan Disamba, sannan suka yi garkuwa da yaransa mata su uku, jaridar ThisDay ta ruwaito.

A cewar idon shaida wanda ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki, ya ce wasu yan bindiga kimanin su 15 sun kai mamaya garin dauke da makamai daban-daban sannan suka fara harbi don tsoratar da mutane.

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe jigon PDP, sun yi garkuwa da yayansa mata su 3
Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe jigon PDP, sun yi garkuwa da yayansa mata su 3 Hoto: Naija News
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Kirsimeti: Ndume ya yi Allah wadai da hare-haren Boko Haram suka kai kauyukan Borno da Adamawa

An ce yan bindigan sun fara kai hari ga yan kasuwa a shahararriyar kasuwar Beji kafin suka zo karamar hukumar Bosso. An ce sun kai ziyara biyu a baya ga jigon PDP a garin.

Koda dai rundunar yan sanda bata riga ta tabbatar da al’amarin ba, wani makusancin marigayin ya ce an shirya kaiwa Alhaji Mohammed hari ne saboda yana da karfi sosai.

“Wannan shine karo na uku da yan bindiga ke kaiwa mutumin harin. Suna ta zuwa a baya amma basu cimma nasara ba saboda mutumin na da karfi. An harbe shi sau da dama kafin ya mutu.”

An binne jigon na PDP a ranar da aka kashe shi daidai da koyarwar addinin musulunci.

KU KARANTA KUMA: Babu shakka Najeriya za ta tarwatse matukar ba a dauka wannan matakin ba, Fitaccen shugaba a Arewa

A wani labarin, wani abun bakin ciki ya riski jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Lagas sakamakon mutuwar Timothy Oyasodun, wani babban jigonta.

Oyasodun, wanda ya kasance malamin addini, ya mutu a ranar Asabar, 26 ga watan Disamba, inda aka bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi ga ahlin APC a jihar Lagas.

Ya kasance Shugaban jam’iyyar mai mulki a karamar hukumar Bariga da karamar hukumar Somolu, jaridar The Nation ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng