Yanzu Yanzu: Hawaye sun kwaranya yayinda Shugaban APC a Lagas ya mutu (hoto)

Yanzu Yanzu: Hawaye sun kwaranya yayinda Shugaban APC a Lagas ya mutu (hoto)

- Mutanen yankin Bariga da ke karamar hukumar Somolu a jihar Lagas sun rasa wani babban danta kuma dan siyasa

- Revered Timothy Oyasodun ya rasu a safiyar ranar Asabar, 26 ga watan Disamba

- Oyasodun, shahararren malamin kirista ya kasance Shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar Bariga

Wani abun bakin ciki ya riski jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Lagas sakamakon mutuwar Timothy Oyasodun, wani babban jigonta.

Oyasodun, wanda ya kasance malamin addini, ya mutu a ranar Asabar, 26 ga watan Disamba, inda aka bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi ga ahlin APC a jihar Lagas.

Ya kasance Shugaban jam’iyyar mai mulki a karamar hukumar Bariga da karamar hukumar Somolu, jaridar The Nation ta ruwaito.

Yanzu Yanzu: Hawaye sun kwaranya yayinda Shugaban APC a Lagas ya mutu (hoto)
Yanzu Yanzu: Hawaye sun kwaranya yayinda Shugaban APC a Lagas ya mutu Hoto: Somolu Voice
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Hadiza Gabon ta gwangwaje tsohon da yace yana sonta

Kafin ya zama Shugaban APC a Bariga, Oyasodun ya kasance sakatare janar na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a kananan hukumomin Somolu da Kosofe.

Da yake martani kan mutuwar jigon jam’iyyar, sanata mai wakiltan Lagas a gabas, Tokunbo Abiru, ya bayyana Oyasodun a matsayin mutum wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen bautawa Allah, al’umma da APC a Lagas gaba daya.

A wani labari, Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan rundunar soji, Sanata Ali Ndume, a ranar Juma’a, ya yi Allah wadai da hare-haren Boko Haram a kauyen Pemi da ke jihar Borno da garin Garkida da ke karamar hukumar Gumbi jihar Adamawa a daren Kirsimeti.

Garin Garkida ya kasance daya daga cikin wuraren da mishan suka fara zama a arewacin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: A lokaci daya 'yan Boko Haram suna kai hari a kauyuka 3 na Borno

Makasan sun badda kamanni a matsayin masu aikin leburanci, a cewar wani dan shekara 24 da ya tsira daga kisan gillar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel