AMAA: Jaruma Maryam Booth ta samu gagarumar lambar yabo
- Sannaniyar jarumar fina-finan Kannywood, Maryam Booth, ta zama gwarzuwar jarumar AMAA
- Hakan ya biyo bayan rawar da ta taka ne a wannan fim din mai suna The MilkMaid
- Jarumar ta wallafa hakan cike da murna a shafinta na Instagram tare da jarumi Ali Nuhu
Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Maryam Booth, ta tabbata a gwarzuwar jarumar Africa Movie Academy Awards, jaridar Daily Trust ta wallafa.
Maryan Booth ta samu nasarar ne sakamakon rawan da ta taka a wani fim mai suna The Milkmaid, inda ta bige Chairmaine Mujeri (Mirage), Linda Ejiofor (4th Republic) da wasu mutane hudu.
A cike da murnar wannan nasarar, jarumar ta wallafa rubutu a shafinta na Instagram kamar haka: "Ina taya kaina da iyalan fim din milkmaid murna. Muna fatan karin nasarori, sai mun hadu nan gaba a Oscar."
KU KARANTA: Alibaba, hadimin Ganduje ya bai wa Kwankwaso hakuri bayan tuhumar da ya sha kan kazafi
Hakazalika, a taya jarumar murnar wannan lambar yabo, fitaccen jarumi Ali Nuhu ya yi wallafa a shafinsa na Instagram kamar haka: "Ina taya ki murna a kan wannan gagarumar nasara a fim din The Milkmaid. Wannan ne tushe, diyata Maryam Booth."
Taron da aka yi ta yanar gizo, jarumi Lorenzo Menakaya ne ya dauka nauyinsa a ranar 20 ga watan Disamban 2020.
KU KARANTA: 'Yar aljanna: Matar aure ta kwarara wa mijinta addu'o'i bayan ya yi wuf da dalleliyar amarya
A wani labari na daban, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa a kan harkar yada labarai, Garba Shehu, ya yi kira ga masu gangamin BringBackOurBoys da su mayar da kudaden da suka karba domin gangamin.
Ya jajanta lamarin tare da cewa babban abun kunya ne garesu da za su yi amfani da satar yaran makaranta da aka yi a Kankara jihar Katsina su tada hankula.
Shehu ya ce wadanda suka kirkiri BringBackOurBoys ba su da kishin kasa, ThePunch ta wallafa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng