Kafin ka nemi auren ƙabilar Ebira: Muhimman abubuwan da ya kamata ka sani

Kafin ka nemi auren ƙabilar Ebira: Muhimman abubuwan da ya kamata ka sani

- Kabilar Ebira ce mafi rinjaye a jihar Kogi kuma Allah ya yi masu kyawawan mata na gani na fada

- Sai dai kamar kowacce kabila, tana da nata al'addun a yayin neman aure

- Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin abubuwan da mutum ya kamata ya sani a yayin neman aurensu

Kabilar Ebira ana samun su ne a jihar Kogi musamman a kananan hukumomi biyar na jihar da suka hada da Okehi, Ajaokuta, Okene, Ogorimagongo da Adavi.

Baya ga jihar Kogi, kabilar sun yadu a fadin wasu jihohin Najeriya musamman a Ondo da Ekiti.

Matan kabilar sun kasance masu tsantsar kyawu kuma cikin sauki hankalin maza ke karkata a kansu. Kyawunsu kadai zai sa mutum ya ji yana kaunarsu a ganin farko.

Kafin ka nemi auren ƙabilar Ebira: Muhimman abubuwan da ya kamata ka sani
Kafin ka nemi auren ƙabilar Ebira: Muhimman abubuwan da ya kamata ka sani Hoto: Jumia Food
Asali: UGC

Sai dai duk da kyawunsu akwai abubuwan da ya kamata ka sani game da su kafin ka auresu. Dalili kuwa shine domin ka shirya kan abunda za a nema daga gareka a lokacin bikin.

KU KARANTA KUMA: 2023: Rikicin cikin gida ka iya sa APC shan kaye a Jigawa, in ji Gwamna Badaru

Ga wasu daga cikin abubuwan:

1. Mafi akasarin mutanen kabilar Musulmai ne wanda hakan ke nufin yawancin kyawawan yan Ebira da kake gani Musulmai ne wadanda suka riki addini sosai, kuma da wuya a sauya su ta dalilin aure.

2. Idan kana son aure daga kabilar Ebira, ba huruminka bane sanar da iyayenta kudirinka. Yayinda wasu da dama ke tunkarar iyayen yarinya kai tsaye don sanar masu da kudirinsu, a al’adar Ebira, magabatanka ne za su aikata hakan.

3. A yayin baiko wanda ake kira da ‘Ise Ewere’ da yaren Ebira, magabatansa ne za su je gidan surukansu don yin wasu al’ada.

Sannan a yayin baikon, magabatan amaryar za su samar da kayan abinci da na sha domin karrama bakinsu.

KU KARANTA KUMA: Hawaye sun kwaranya yayinda tsohon gwamnan Nigeria ya mutu

A yayin baikon kuma, magabatan angon za su samar da wasu kayayyaki kamar haka:

Doya guda 100

Bushasshen kifi da naman daji

Lemukan sha

Goro

Man ja

Buhun gishiri

Man gyada

Sarkoki na amarya

Tufafin sawa a cikin jaka na amarya

Zanuwa biyu na amarya (ba dole bane)

Kudi na magabata

Wasu daga cikin wadannan kayayyaki ba dole bane bisa ga al’ada saboda ya danganta da ra’ayin yan uwan amaryan. Idan suka ga dama suna iya soke kayayyakin.

Wani abu kuma da za a lura game da kayayyakin shine, ana raba mafi akasarinsu ne ga yan uwa da makwabta domin su sanyawa amaren albarka.

4. Kudin sadaki

Magabatan amarya ne ke yanke kudin sadaki kuma mafi yawan lokuta su kan duba karfi da wadatan angon ne.

Sai dai kuma akwai wasu kudade da wajibi ne a biya su bisa ga al’ada, kamar:

1. OZEMEIYI: Wannan kudi ne da ake biya don tabbatar da cewar angon na muradin amaryar.

2. OTANUVOGE: Wannan shine kudin da ake biya domin hada hannayen ma’auratan a waje daya.

3. IDOZA: A lokutan baya, mutumin da ke son auren yarinya dole ya taimakawa surukansa a gona amma a yanzu, kudi ake biya a madadin haka. Kudin da za a biya saboda haka shine Idoza.

Mun samu wannan cikakken bayani ne a wani wallafa da shafin Arewa RantHQ yayi a Facebook.

A wani labari, Shahrarren attajirin jihar Katsina, Dahiru Mangal, ya bada gudumuwar sama da motoci 100 ga yakin neman zaben tsohon minista, Mohamed Bazou, a jamhurriyar Nijar.

A wani bidiyon da PRNIgeria ta samu, attajirin ya bayar da motocin ne a garin Maradi, wacce ke da iyaka da Najeriya.

An yi rubutu “Mohammed Bazoum, 2021” a jikin motocin hade da hotunan dan takaran.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel